✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta kashe dakarun sa-kai 8 a Borno

Galibi ’yan ta’addan sukan dasa nakiyoyi a kan hanyoyin da suka san jami’an tsaro na bi wajen farautar su.

Akalla dakarun sa-kai na Civilian JTF 8 ne suka mutu sakamakon taka wani bam da mayaƙan ISWAP suka dasa a Karamar Hukumar Gamboru ta Jihar Borno.

Bayanai sun ce waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan hanyar zuwa Maiduguri daga Gamborun Ngala nan take sun mutu bayan sun taka wata nakiya da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka binne a ranar Asabar.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa ƙwararren masani kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama cewa wasu mutane uku da abin ya shafa sun samu raunuka daban-daban.

An kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti yayin da dakarun sa-kai takwas da suka mutu an yi musu jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Wannan mummunan aika-aika na kwantan bauna da ’yan ta’addan ISWAP ko Boko Haram ke gudanarwa ba shi ne karo na farko ba.

Aminiya ta ruwaito cewa kusan a kan samu faruwar makamancin wannan lamari lokaci zuwa lokaci.

Galibi dai ’yan ta’addan sukan dasa nakiyoyi a kan hanyoyin da suka san jami’an sojoji da na sa-kai na bi wajen farautar su.

Wannan lamari ya sanya a kodayaushe masana harkokin tsaro ke gargaɗin jami’an tsaron da su riƙa taka-tsan-tsan yayin sintirin da suke don kaucewa fadawa tarkon waɗannan ’yan ta’adda.