✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ce ta kai hari a cocin Ondo – Gwamnatin Tarayya

Ministan Aregbesola ne ya bayyana haka a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce ’yan ta’addan kungiyar ISWAP ne suka kai hari kan Cocin Katolika da ke garo Owo na Jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, lokacin da yake yi wa manema labaran Fadar Shugaban Kasa jawabi, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne dai ya jagoranci taron a Fadar Aso Rock da ke Abuja, a ranar Alhamis.

Ya ce gwamnati ta sami nasarar gano wadanda suka kai harin, inda ta tabbatar da cewa mambobin kungiyar ISWAP ne.

Aregbesola, wanda ya yi jawabin a gefen Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce tuni aka umarci jami’an tsaro su zakulo masu hannu a cikin harin don ganin an hukunta su.

Ministan ya ce ’yan ta’addan na kokarin harzuka ’yan Najeriya ne su ci gaba da karkashe juna ta hanyar kabilanci da addini sanadiyyar harin.

Akalla mutum 40 ne Gwamnatin Jihar ta Ondo ta tabbatar da rasuwarsu a harin wanda aka kai shi lokacin da mutane suke tsaka da ibada, wasu kuma da dama suka jikkata.