Jiragen sama na yaki mallakar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a Arewacin Zirin Gaza.
Jiragen sun kai hare-haren kan wasu wurare da ke unguwar Bayt Lahiye.
Babu wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta fitar game da hare-haren.
A gafe guda sanarwar da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ta ce, a hare-haren an nufi cibiyoyin kungiyar Hamas kuma an yi hakan ne don mayar da martani ga hari da makamin roka da aka kai wa Isra’ila daga Zirin Gaza.
Sanarwar ta kara da cewa, wuraren da aka kai harin mallakar sojojin Hamas ne.