✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Irin dimokuradiyyar Najeriya ke nan

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan damben ’yan Majalisar Najeriya, wadanda aka zaba kan tafarkin dimokuradiyya. Irin dimokuradiyyar Najeriya ke nan yau…

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan damben ’yan Majalisar Najeriya, wadanda aka zaba kan tafarkin dimokuradiyya. Irin dimokuradiyyar Najeriya ke nan yau ga shi ’yan Majalisar Nijeriya na dambe da kokowa a Zauren Majalisa har da yage-yagen riguna wanga abin kunya har ina ace wai mun kasa bambanta ’yara ’yan aji daya na makarantar Firamare da ’yan Majalisar Najeriya. Don haka ’yan PDP ku sani fa gudu da mari bai hana yin bauta.
Daga Zaidu Bala Kofar Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya. 07037697009.

Sakonnin waya

Martani ga Maryam Abdurrasheed
Editan don Allah ka ba ni fili in yi wa ’yar uwata martini kan cewa ki sani ba dukkan wakokin yabo ba ne shirka, domin shirka ita ce hada Allah da wani. Wannan kuskure ne, domin wasu har kafirta mutane suke yi. Ni ma ina kira ga irin wadannan mawakan da su sana bin da za su rika furtawa. Daga Kawulle Kaduna 08052659678.

Ga Gwamnan Borno
Assalamu alaikum. Aminiya ku isar min da kukana ga Gwamnan Borno, Kashim, a taimake mu a sake mana ’yan uwanmu a Giwa Barack, domin muna halin maraici. Allah Ya kawo mana zaman lafiya amin. Daga Abbaniye Maiduguri 07063232385.

Nawa ne farashin Aminiya?
Aminiya ki fada mana farashinki, mu dinga biya, saboda ba kya so ki isar mana sakoninmu. Ga gaisuwa nan zuwa ga Gwamnatin Jihar Kano ta musamman zuwa ga Hon. Isyaku Ali danja da Hon Musa Ado Tsamiya Babba da Hon Sha’aibu Idris Zango da Hon. Chairman Ibrahim Isah Jogana da duk ’yan kungiyar ci gaban PDP na Gezawa. Daga Nasiru Isiyaku K. Kudi Gezawa 080224825952/08091315817.

Ko za ka  buga sakona?
Edita na turo sako a wani mako ba ka buga ba, don haka  na sake turowa in gani ko za ka buga a wannan makon. Daga Sadik Nazir Gwagwalada 080861513864.

Mene ne laifin ’yan garuwa?
Hana goyon babur mene ne amfanin haka? Kuma mene ne laifin ’yan garuwa a Kano? An hana mu ruwa, an kuma hana amsu saida ruwa adalci ke nan? Daga 08032202069.

Kan talakawa ya waye
Aminiya abar katsalandan da shiga abin da babu ruwanku naji an yi tsokaci kan a watsar da maganar Janar uban talakawa, a yi koyi da halinsa kawai. Wannan ba amfita ce ba. Ku sanar da shugabannin Najeriya cewa talakawa kansu ya waye, 2015 za su sha kallo. Daga Muhammad Hassan Daura 08069470608.

Sako ga Ganduje
Aminiya jaridar talakawa, Edita ka ba ni dama in yi kira a Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Maigidanka ba ya kaunar talaka, kuma duk abin da za a yi na gallaza wa talaka kai yake aika. Lokaci ya yi da za ka yi hangen nesa. Daga Hafizu Sabi’u danladi Brigade Gama C Kano. 08066551055.

Jinjina ga APC
Aminiya a mika fatan alherina ga ’ya’yan jam’iyyar APC. Ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi. Allah Ya kawo mana karshen mulkin kama-karya da mulkin zalunci. Daga Babangida Ibrahim Gora Mile 12, Legas 08058365986.

Ga AbdulWahid Omar
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, AbdulWahid Omar in dai ga gaskiya, muna goyon bayanku dari bisa dari, saboda ’yan Najeriya adalci suke so. Daga Yahaya A. Jauro, Jayi II Katampe, Abuja 08077085505.

Allah Ya jikan Amadu Na-Funtuwa
Tun ranar da Amadu na Funtuwa ya yi wafati a garin Kaduna, har yau ba a samu wani mutum wanda ya ci gaba da aikin alherin da Na-Funtuwa ya rasu ya bari ba. Wannan babban kalubale ne. Yanzu wacce hanya ake bi don gano ’yan uwan mutane da hadari ya rutsa da su, suka rasu. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.

Mu ji tsoron Allah
Edita ka ba ni dama in yi kira ga al’ummar Musulmi, a wannan jarida mai albarka da filinmu na wasikun tes, in yi kira ga al’ummar Musulmi, mu ji tsoron Allah, mu kiyayi zalunci. Komai za mu aikata, mu yi don Allah. Mu tuna za mu mace, mun zam gawa, Allah Zai yi mana hisabi. Allah Ya shiryar da mu. Daga Usama Usman (Kawulle) 08052659678.

Ga Mujahid Dokubo
Editan Aminiya gaya wa Asari Dokubo ga shi da suna mai kyau na Mujahid, amma zuciyarsa baka kirin. Tunaninsa na nuni da rashin imani. Don haka muna rokon Allah tsari daga sharri da bala’in da ya ke nufin Najeriya da shi. Daga Zauro Abdullahi Sakkwato 08069077363.

Siyasar addini ta rage
Siyasar gurguzu ta rushe, dimokuradiyyar Amurka ta rushe, sai ta Musulunci, Siyasa Islamiyya, wadda ke hani da mummuna, ta yi umarni da kyakkyawa; babu angar siyasa da zage-zagen adawa ko zanga-zangar tawaye. Allah Ya dora mu kan tafarki madaidaici. Allah Bai halicci mutum da aljanni ba, sai don su bauta masa.Daga 08060116666.

’Yan Arewa suka wulakanta kansu
Akasarin mawadata ’yan Arewa ko da masu bara a titin sun fi su, domin ko zakka bas a son fitarwa kamar yadda Allah Ya umarce su da yi. Sarakuna da attajirai da Malamai ba su wuce cima zaune ba, a gurin mutanen Kudu. Matasa sun zama dilallai na masu neman mulki, ba tare da rashin mutuncinsa ba, ko kimar asalinsa ba. Ana ta kisan rayuka ba a biyan diyya. Daga AbdulKareemu dayyabu.

Ina rahoton Jibiya
Aminiya wai Jibiya ko ba ta cikin tsarinku ne, don taba ganin rahotanta ba. Daga Idris Magama Jibiya 07038237530.

Direbobi a yi hakuri
Assalamu alaikum. Aminiya ku ba direbobin manyan mota hakuri da cutar da ma’aikata suke mana, a hanyar Fatakwal. Daga Aliyu Abubakar Jos Ali Kazaure. 08036565554.

Jinjina ga Shema
Aminiya ku ba ni dama in mika godiyata ga Gwamnanmu na Katsina a kan kokarin da yake na ganin ya kawar da matsalar kauraye a cikin gari da kewaye da fatan Allah Ya kara taimakawa. Amin. Daga Ibrahim KSD 08031944943.

Ga Mawaki Haruna Aliyu Ningi
Ka kyauta da ka yaki PDP, inda ka nuna wa mutane illar uwar da ke halaka ’ya’yanta a cikin baitukan wake. Allah ya kara basira. Daga Danso Fatara Azare. 08136746876.

Nesa ta zo kusa
A fahimtata Jonathan zai fi son ya samu hadin kan duk gwamnonin da suke yin rigima da shi, fiye day a yi rigima das u. Abin bakin ciki bai wuce talakawa da suka kasa yin katabus ba, a kan hakkinsu, duk da irin talaucin day a yi musu katutu. Ga sanatoci da wakilai babu abin da suka rasa, amma suna yin fito na fito da shugaban kasa, a kan zaluncin rashin tsaro, ga barazanar masu satar gurbataccen mai. Mu yunkura za mu hadu d ataimakon Allah, cikin yardarSa. Daga Abdu 08060116666.
Yabo ga Aminiya
Zuwa ga Editan jaridar Aminiya.   Da fatan kuna cikin koshin lafiya.  Hakika
kun cancanci yabo bisa namijin kokarinku na dauko labarai birni da kauye, domin ilmantarwa da fadakarwa da kuma nishadantarwa.  Hakika dukkannin ma’aikatanku kwararru ne a wajen aiki da iya ma’amalla.  Don haka nake cewa Allah Ya taimaki Aminiya jaridar kwarai.  Daga Amininku Yahaya Muhammad  Maina  Maina Scraps And Fishery Keeping Com.