Iran ta yi kakkausar suka game da tashin hankalin da ke gudana kan al’ummar Musulmi a Indiya.
Ministan harkokin wajen Iran din, Javad Zarif, ne ya yi wannan sukar a shafinsa na Twitter.
Zarif, ya ce Iran ta kasance kawar Indiya shekaru aru-aru da suka gabata don haka take kira ga mahukuntan Indiya da su tabbatar da walwalar kowa ne dan kasar tare da taka birki ga ayyukan miyagu wadanda ke cin karensu babu babbaka a tashin hankalin da ke bazuwa a kasar.
Mista Zarif, ya kara da cewar tabbatar da doka da oda da kuma tattauna zaman lafiya su ne kadai za su haifar da duk wani ci gaba.
Idan dai za a iya tunawa, rikici ya barke tsakanin mabiya addinin Hindu da al’ummar Musulmin a birnin Delhi na Indiya a ranar 23 ga watan jiya.
Rahotanni sun ce, mabiya addinin Hindu sun kona gidaje da shagunan Musulmin Indiya.