Kasar Iran ta kwace Fasfon Ali Daie, tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar, a bisa sukar gwamnatin kasar.
A cewar wasu rahotanni na kafofin yada labaran kasar, Ali Daei ya janyo wa kansa fushin gwamnati ne sakamakon sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a kan zanga-zangar da ake yi a kasar kan mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da ake zargin an kashe sakamakon jagorantar fafutikar bai wa mata damar fita babu hijabi ko kallabi.
- Rashin lafiya ne ya kashe Mahsa Amini, ba ’yan Hisbah ba —Iran
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 22 a Iran
Haka kuma, Ali Daie ya yi tsokaci kan yadda hukumomin kasar ke murkushe masu zanga-zanga kan dokar hijabi, lamarin da ya bayyana a matsayin ‘murkushe wa da karfin tuwo’.
A ‘yan makonnin da su ka wuce ne fitaccen dan kwallon ya yi kira ga Gwamnatin Iran da ta “yi kokarin magance matsalar ‘yan kasar ta hanyar da ta dace, ba ta yi amfani da tursasa wa, da kamen jama’a maras dalili ba.”
Ali Daei na daya daga cikin ‘yan kasar Iran na farko da suka buga kwallo a Gasar Zakarun Turai, bayan da ya buga a Bundesliga da kungiyar Arminia Bielefeld kafin ya koma Bayern Munch da kuma Hertha Berlin.
Ali Daie dai shi ne yake rike da tarihin wanda ya fi kowa cin kwallaye a wasannin kasa da kasa da ya buga, inda ya ci kwallaye 109 kafin Cristiano Ronaldo ya karbe kambun a watan Satumbar 2021.