✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta kakaba wa wasu mambobin EU takunkumi

Takunkumin ya hada da haramta musu biza da kuma kwace dukiyoyi da kadarorinsu.

Iran ta sanar da kakaba takunkumi kan cibiyoyi da daidaikun mutane da kafafen yada labarai da ke kasashen Kungiyar Tarayyar Turai.

Wannan dai wani martani ne ga matakan ladabtarwa da EU ta dauka kan masu murkushe zanga-zanga a kasar.

Wasu ‘yan Majalisar Dokokin Faransa da kuma manema labarai biyu na jaridar Bild ta Jamus na daga cikin wadanda gwamnatin Iran ta sanya wa takunkumi.

A cikin sanarwar da ta fitar a birnin Tehran, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta zarge su da goyon bayan ’yan ta’adda tare da haddasa tashin hankali a kasar.

Takunkumin ya hada da haramta musu biza da kuma kwace dukiyoyi da kadarorinsu a yankin da ke karkashin ikon Iran.

Wannan mataki ya zo ne mako guda bayan da Iran ta fara sanya takunkumi kan wasu jami’ai da hukumomin Birtaniya, bayan da Landan ta kakaba wa ’yan sandan da’a na Iran takunkumi saboda mutuwar Mahsa Amini.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dubban mutane suka taru a kabarin matashiya Mahsa Amini a yankin Kurdistan domin yi mata adu’o’i na karshen makokin kwanaki 40 da aka saba a Iran.