✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPOB: ’Yan kabilar Ibo sun rufe shaguna a Jos saboda fargaba

Kananan rigingimu na mazauna birnin kan rikida zuwa tarzomar addini da na kabilanci.

’Yan kabilar Ibo da ke kasuwanci a Jos, babban birnin Jihar Filato, sun rufe shagunansu saboda fargabar harin ramuwar gayya sakamakon abin da ke faruwa a yankin Kudu maso Gabashin Kasar. 

’Yan awaren Biyarafa (IPOB) na ci gaba da kai hare-hare a wasu jihohin na Kudu maso Gabashin kasar musamman a kan gine-ginen gwamnati.

Wakilinmu ya ruwaito galibin ’yan kabilar Ibon masu harkokin kasuwanci a kwaryar birnin Jos ba su bude wuraren kasuwancinsu ba a safiyar Litinin. 

Mutane da dama wadanda suka riga suka bude tun farko daga bisani sun rufe da rana. 

Wakilin namu wanda ya kewaya kan titin Ahmadu Bello da Kasuwar Katako da sauran wurare a cikin birnin, ya ce ko baya ga ‘yan kabilar Ibon wadansu ‘yan kasuwar ma sun rufe saboda tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo idan rikici ya barke a birnin. 

Kazalika, rahotanni sun tabbatar da ganin jami’an tsaro masu dimbin yawa da aka girke a kan titin na Ahmadu Bello, domin tarar numfashin duk wata tarzoma da ka iya tashi a yankin da ma sauran wurare a babban birnin jihar. 

Aminiya ta fahimci cewa daukar matakin da jami’an tsaron suka yi cikin hanzari bai rasa nasaba da azamarsu ta kare aukuwar rikicin kabilanci da na addini a birnin Jos da kewaye.

A lokuta da dama, kananan rigingimu da rashin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu na mazauna birnin kan rikida zuwa tarzomar addini da na kabilanci.