Duk da sanya la’adar Naira miliyan 10 don kamo wadanda suka kashe dan majalisa a Jihar Anambra, haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara (IPOB) ta sha alwashin ci gaba da kashe su daya bayan daya.
A karshen makon nan ne dai wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar ne suka fille kan dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguata II a Majalisar Dokokin Jihar, Okechukwu Okoye, tare da hadiminsa, Cyril Chiegboka.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget
- Duk da kukan talauci talakawan Najeriya na kara kiran waya
Dan majalisar dai shi ne ke wakiltar mazabar da Gwamnan Jihar, Farfesa Charles Soludo ya fito.
IPOB dai ta yi wannan barazanar ce a cikin wata wasika da aka tsinta a kusa da inda ta jefar da kan marigayi dan majalisar.
Wata majiya da ta ga wasikar ta ce, “Rubutun wasikar bai fito sosai ba saboda ruwa ya taba ta, amma ta fara da kalmar ‘gargadi’ ne.
“Sannan a wani wurin ta ci gaba da cewa duk inda kuka shiga, ba za ku boye mana ba, sai mun cim muku daya bayan daya, saboda yanzu sojoji da ’yan sanda ba su ne matsalar mu ba.”
Kisan mutane da kone dukiyoyinsu dai na ci gaba da karuwa a Jihar a ’yan kwanakin nan.
Akalla hedkwatar Kananan Hukumomi Hudu ne da ofisoshin ’yan sanda da dama aka kai wa hari wasu kuma aka kone su kurmus.
Aminiya ta rawaito cewa Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan 10 a matsayin la’ada ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kamo wadanda suka aikata kisan.
A ranar 15 ga watan Mayun 2022 ce aka sace dan majalisar tare da hadiminsa, sai dai a ranar Asabar din da ta gabata an tsinci kanshi a garin Nnobi da ke Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a Jihar ta Anambra.