Dokar zaman gida na tilas da haramtacciyar kungiyar ‘yan aware ta IPOB ta gidanya, ya samu karbuwa a kusan dukkanin biranen Jihar Anambra.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, mazauna sun amsa kiran a garuruwan Awka, babban birnin jihar da Onitsha cibiyar kasuwanci har ma da yankunan Nnewi da sauransu.
Daga cikin wadanda suka amsa kiran har da bankuna da ofisoshin gwamnati da ma ma’aikatu masu zaman kansu a cikin jihar.
Masu aiko da labarai sun ce kusan za a iya cewa shaguna da kasuwanni da otel-otel duk sun kasance a garkame.
Makarantun sakandaren gwamnati da na masu zaman kansu da gidajen mai da ma masu sana’o’in hannu duk sun kasance a rufe.
Rahotannni sun nuna cewa dukkanin hanyoyin da ke danganawa da Jihar ta Anambra sun zama kufai yayin da jama’a suka bi umarnin zaman gida na tilas da kungiyar ta gindaya.
Sai dai wakilin Aminiya ya ce ya shaida yadda aka jibge jami’an tsaron hadin gwiwa na sojoji da takwarorinsu a kan manyan titunan domin tabbatar da bata-gari ba su yi amfani da wannan dama ba wajen karya doka da oda.
Kazalika, jami’an tsaron suna kokarin tabbatar da ma’aikatan da ayyukansu suka zama na wajibi kamar manema labarai da likitoci da nas-nas da sauransu, an ba su damar danganawa zuwa wuraren aikinsu.