Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN), ta buƙaci matatar Dangote da ta rage farashin litar man fetur da ta ke sayar wa dillalai daga Naira 970 zuwa ƙasa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa farashin dakon man daga ƙasashen waje ya sauka zuwa Naira 900.28 kan kowace lita.
- Abba ya bai wa Sani Danja muƙamin mai ba shi shawara
- ECOWAS ta shiga taro bayan ficewar Nijar, Mali da B/Faso
Mai magana da yawun IPMAN, Chinedu Ukadike ne, ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar Punch.
Ya ce rage farashin zai taimaka wajen rage wa ’yan ƙasa wahala.
Chinedu, ya ƙara da cewa farashin samar da mai ya bambanta daga matata zuwa matata, amma ya ce akwai buƙatar matatar Dangote ta sake nazari kan farashin da ta ke sayar da litar mai ga dillalai.
A watan Nuwamba, matatar Dangote ta rage farashin litar man fetur daga Naira 990 zuwa Naira 970 don nuna godiyarta ga al’ummar Najeriya kan goyon bayan da suke ba ta.
Wannan ya faru ne a lokacin da ake raɗe-raɗin cewa za a ƙara farashin man fetur a Najeriya.
A watan Yuli, Shugaba Bola Tinubu, ya shawarci majalisar zartarwa ta ƙasa cewa a fara sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida irin su Dangote da sauran su a kuɗin Naira.
Majalisar ta amince da wannan shawarar, tare da yanke hukuncin sayar da gangar mai 450,000 ga matatun cikin gida da dillalan mai ta wannan tsarin.