Ƙungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa ta Ƙasa (IPAC), reshen Jihar Katsina, ta bayyana amincewarta da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Laminu Lawal Boyi, ya bayyana cewa IPAC ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da bai wa dukkanin jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen.
- Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan sanda a Ondo
- NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya
“Baya ga shugabancina a IPAC, ni kuma shugaban jam’iyyar Accord ne, wacce ta shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 34 da kujerun kansiloli 361 a faɗin jihar.
“A matsayina na ɗan takara kuma mai ruwa da tsaki, na gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen,” in ji shi.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ofishin IPAC da ke Kofar Durbi, a cikin garin Katsina, tare da wasu jiga-jigan ƙungiyar, Alhaji Laminu ya jaddada cewa a kowane zaɓe dole ne a samu wanda zai yi nasara da kuma wanda ba zai yi ba.
Ya yi kira ga waɗanda ba su yi nasara ba da su karɓi ƙaddara tare da duba gaba, domin siyasa ba ta ƙarewa.
Haka kuma ya shawarci waɗanda suka yi nasara da su fahimci cewa nasarar ba daga ƙarfinsu ko dabara ta fito ba, sai dai hukuncin Allah ne.
Don haka, ya buƙace su da su sauke nauyin da ke kansu cikin adalci, ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, domin yanzu lokaci ne na haɗin kai da ci gaban al’umma gaba ɗaya.
Alhaji Laminu ya ƙara da cewa, “Yanzu siyasa ta wuce, lokaci ne na aiki da tabbatar da ci gaban jama’a.
“Waɗanda suka samu nasara su yi mulki da adalci, su guji nuna bambanci, domin yanzu dukkanin al’umma na kallonsu a matsayin shugabanninsu, ba wai na jam’iyyarsu kaɗai ba.”
Shugaban ya yaba wa dukkanin ’yan takara da jam’iyyun siyasa da suka shiga zaɓen, tare da gode wa hukumomin da suka shirya zaɓen bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da gudanar da shi cikin zaman lafiya da lumana.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa shugabanni goyon baya domin ci gaban Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.