Injiniya Aminah Ebimari Sa’idu tana daya daga cikin Injiniyoyi mata kalilan wadanda suka samu takardar shaidar kwarewa a fannin Injiniya a jihar Neja. Ma’aikaciya ce a Ma’aikatar Aiyuka ta Jihar Neja da take sashen kula da gine-gine. Injiniya Aminah ita ce take rike da mukamin Ma’aji a kungiyar Injiniyoyi ta kasa reshen jihar Neja, sannan kuma Sakatariyar kudi ta kungiyar Masana Fasahar Injiniya ta Najeriya, sannan kuma Mamba ce a kungiyar kwararrun Injiniyoyin hanyoyi.
TARIHINA
An haife ni ne shekaru 38 da suka wuce a jihar Legas. Sunan mahaifina malam Musa Sa’idu.Mu biyar ne a wurin iyayenmu,kuma ni ce babba. A nan na fara karatun firamare.Bayan na kammala sai na tafi makarantar sakandare ta Gwamnatin Tarayya ta ’Yan mata da ke garin Bidda. Na je makarantar Koyar da Fasahar kere-kere ta Gwamnatin Tarayya da ke Bidda inda na sami takardar shaida a fannin injiniya. Ban yi kasa a gwiwa ba,na je Jami’ar Bayero da ke Kano don kara karatu inda Allah Ya ba ni sa’a kwalliya ta biya kudin sabulu.
Dalilan da suka sa na yi nazarin fannin injiniya
Koda yake ba wannan fannin na yi niyyar nazari ba tun farko.Na yi niyyar nazarin fannin Likita ne bisa la’akari da muhimmancin rayuwar al’umma,sannan ina matukar sha’awar irin tufafin da Likitoci suke sakawa launin fari,da kuma yadda suke gudanar da harkokinsu.A lokacin ina ta tunanin yadda zan taimaka wa mata musamman idan suka zo haihuwa bisa la’akari da karancin Likitoci mata da ake fama da su a wannan shiyyar ta mu. Da na tinkari mahaifina da wannan burin nawa, sai ya nuna mini ina iya ba da gudumowa irin ta likitoci a fannin injiniya. Ya kara mini da wasu bayanai da hujjojin da suka gamsar da ni,nan take na ji kawai ina sha’awar nazarin wannan fannin da na samu kaina na injiniyan gine-gine.Da haka ni kuwa na yi wa mahaifinmu alkawarin zan iya.
kalubalen da na fuskanta a wannan fannin
Babban kalubalen da na fuskanta yayin nazarin wannan fannin shi ne yadda maza ’yan uwana suka kasance sun fi mata yawa baki daya. Bayan haka, suna yi mana kallon ba za mu kai labari ba don sun nuna mana cewa nazarin fannin ba na mata ba ne, hatta malamanmu sun raina mana kura.Sai da tafiya ta fara nisa ne suka yi la’akari da cewa mun tsaya da kafafunmu ba tare da neman taimakonsu yadda suka yi tsammani ba,daga bisani ma, mu muka rika taimaka wa wasu da bayanai da kuma ayyukan gidan da aka yi ta ba mu a lokacin.
Da na idar da karatu, na yi tsammanin ba zan fuskanci kalubale ba, ashe ba haka abin yake ba,da na kama aiki,a nan ma abokan aikina suka rika yi mini kallon karatun karya na yi, wato ba zan iya aiki ba idan aka kai ni wurin aikin. Babban abin da ya ba su mamaki shi ne, yadda suka ga na zage dantse ina aikina yadda ya kamata.
Dalilan da suka sa na shahara
Gaskiya shaharata ni kaina tana ba ni mamaki, don ni ban yi nazarin wannan fannin don in shahara ba. Shaharata ta farko ita ce, na kasance daya daga cikin mata kalilan wadanda muke da kwarewa a wannan fanni na injiniyar gine-gine.Bayan haka, na kasance mace ta farko a ma’aikatar da na samu takardar shaida ta kwarewa da Hukumar Kula da kwararrun Injiniyoyi [COREN] ta ba ni, bayan da na na samu nasarar jarrabawar da na zauna.
Bayan haka,ba na shiri da al’amarin rahisin gaskiya a duk lokacin da aka ba ni alhakin duba ayyukan da suka hada da samar da hanyoyi da gadoji a sassa daban-daban na jihar Neja. Ka ga a halin yanzu ina duba aikin hanyar da ta tashi daga kauyen Lapai Gwari zuwa Jami’ar kere-kere ta gwamnatin tarayya da ke gidan kwano. Na nemi a yi aikin da ya kamata ta yadda jama’a za su dade suna cin moriyar aikin da Gwamnati ta kashe makudan kudi. Kuma na yi alkawarin aiki tsakanina da Allah da kuma ka’idoji da sharuddan da kungiyarmu ta shimfida.
kasashen da na ziyarta
kasashen da na ziyarta sun hada da Birtaniya da Saudiyya da Jumhuriyyar Benin. Na yi matukar karuwa da abubuwa da dama da na je wadannan kasashen musamman al’amarin da ya hada da ba mu horon kara kwarewa dangane da aikinmu mai matukar tasiri ga al’umma.Gaskiyar malam Bahaushe da ya ce, ‘Tafiya mabudin ilimi’.
Lokutan da ba zan manta a rayuwata ba
Ba zan manta da lokacin da na karbi takardar shaidar kammala ilimin digiri na farko ba,sai lokacin da na karbi takardar shaidar kwarewar a fannin injiniya ta COREN.Sannan lokacin da na hadu da Gwamnan jihar Neja bayan da na sami takardar shaidar COREN.Haka kuma lokacin da na auri mijina da Allah Ya albarkacemu da ‘ya’ya biyu .
Harkokin kungiyoyi
Shiga harkokin kungiya yana daya daga cikin hanyoyin da za ka hadu da jama’a sosai ku yi mu’amala da su musamman abin da ya shafi irin ayyukan da muke yi sun shafi rayuwar jama’ar birane da kauyuka.Wannan ne ya sa na zama ’yar kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya reshen jihar Neja, inda a halin yanzu nake rike da mukamin Ma’aji.Sai kuma kungiyar kwararrun Injiniyoyi ta Najeriya masu fasahar hanya,inda nake rike da mukamin Sakatariyar kudi.Haka kuma ni mamba ce a kungiyar Injiniyoyi masu Gina Manyan Hanyoyi a Najeriya.
Abinci da abin sha
Na fi sha’awar abincin da suka hada da sakwara da miyar agushi, sai shinkafa dafa duka da salad. Abin sha kuwa na fi son fayrouz da juice.
Sutura
Ni musulma ce,sannan kuma ina matukar alfahari da wannan addinin nawa.Ya bayyana mana irin suturun da suka kamata maza da mata su rika amfani da su,don haka tufafin da na fi sha’awa su ne duk wadanda suka cika sharuddan addinin islama.Ina kuma kyamar duk wadanda suka saba wa sharuddan addinina.
Ra’ayi game da ilimin ‘ya mace
Neman ilimi dole ne a kan kowane musulmi, namiji, da mace, yaro da babba yadda Annabin Rahama Muhammadu dan Aminah da Abdullahi ya nuna a hadisinsa.Don haka bin umurnin ya zama dole.Abin da zan gaya maka a nan shi ne,ba ni da wani ra’ayi nawa game da neman ilimin ’ya mace da ya zo sabanin wanda addinina ya bayar da umurni a kai.Duk wanda yake da hannu wurin hana’ya mace samun ilimi, a ganina yana adawa ne da addinin islama.
Yadda nake hutuwa
Babbar hanyar da nake hutuwa ita ce,in zauna a gida musamman ranakun hutun karshen mako tare da maigidana da ’ya’yanmu,mu yi da’ira a falo muna raha, wasu lokutan muna kallon fina-finan da muke sha’awa. Bayan haka, mukan fita mu dan zaga gari tare da zuwa ziyarar ’yan uwa da abokan arziki. Yin haka yana sa mini kara kaunar iyalina fiye da yadda kake tsammani.A duk lokacin da na sami kaina a wani wuri da ba a gida ba,nan da nan nake kewar kowa a gidan musamman maigida da yarana.
Burina
Babban fatana shi ne yadda Allah ya raya ni a cikin addinin islama,ya sa in ci gaba da bai wa addinin gudunmawa tare da yin hidimar da al’umma za ta ci gaba a kowane lokaci. Ina kuma so in zama abin koyi ga al’umma.