Tsuntsaye sun yi wa jirgin kamfanin Max Air kutse a sararin samaniya, suka lalata wani bangare na injin din jirgin.
Max Air ya ce lamarin ya faru ne bayan tashin jirgin daga Kano zuwa Abuja a ranar Talata, kuma matukin jirgin ya dauki matakin kandagarki, ya juya zuwa Kano bisa tsari da shawarar da ake bayarwa a harkar sufurin jiragen sama.
- An yi garkuwa da alkali a cikin kotu
- ’Yar shekara 6 ta mutu sakamakon fyade a Kaduna
- Hisbah ta kama mutum 6 da kwalaben giya 500 a Jigawa
“A lokacin da jirgin ke tashi, mun gamu da kutsen tsuntsaye zuwa cikin injin dinsa na biyu, suka lalata wani bangarensa,” inji Daraktan Kula da Jiragen Max Air, Injiniya Muhammed Mubaraq.
Da yake musanta ikirarin da ke cewa fasinjojin sun tsallake rijiya da baya, ya yi bayani cewa, “Matukin jirginmu ya bi ka’ida yadda ya kamata sannan ya juya da jirgin, ya sauka.”
Ya kara da cewa an sauko da fasinjoji lafiya ba tare da wani hadari ko tangarda ba.
“Bayan saukarsa, injiniyoyi sun duba lafiyar jirgin, suka maye gurbin abin da ya lalacen. Sun gudanar da aikin yadda ya kamata, sannan suka saki jirgin.
“A yanzu da nake magana da ku, jirgin ne na hau zuwa Abuja. Ba daidai ba ne a ce sun tsallake rijiya da baya,” a cewarsa.
A cewarsa, babu wani bakon abu mara kyau da ya faru saboda kutsen tsuntsaye cikin injin jirgi ya zama ruwan dare, kuma matukin jirgin ya yi abin da ya dace ta hanyar karkata akalar jirgin.