✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Injin janareta ne ya jawo gobara a Kasuwar Sabon Gari’

A ranar Talatar da ta gabata ne gobara ta tashi a Gidan Maggi a Kasuwar Sabon Gari da ke Jihar Kano, inda ta cinye wani…

A ranar Talatar da ta gabata ne gobara ta tashi a Gidan Maggi a Kasuwar Sabon Gari da ke Jihar Kano, inda ta cinye wani bangare na gidan kafin daga bisani ’yan kwana-kwana su samu nasarar kashe ta.

Aminiya ta zanta da Malam Amadu Sani wanda abin ya faru kusa da rumfarsa, inda ya bayyana cewa wani karamin injin samar da hasken lantarki ne ya yi sanadiyyar tashin gobarar
kuma babu asarar rai sai dai wani mutum guda ya sami rauni sakamakon dirowa da yayi daga saman gidan da gobarar ta tashi.
Daraktan Hukumar ’Yan Kwana-Kwana ta jihar, Alhaji Balarabe Kabara ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne sanadiyyar injin janareta kuma tuni mutanen sa sun sami nasarar dakile wutar tare da hana ta ci gaba da yaduwa zuwa sauran bangarorin kasuwar.
Wani dan kasuwa da wakilinmu ya zanta da shi ya ce: “A mafiya yawan lokuta ana samun tashin gobara a kasuwanni saboda yawaitar kananan injuna a ko’ina sannan akan ajjiye su cikin kayayyaki masu saurin kama wuta kamar kwalaye da ledoji da kuma tsummokara.”