Tawagar kwallon kafar mata ta Ingila ta yi waje da ta Najeriya a matakin sili daya kwale na Gasar Kofin Duniya ta 2023 da ke gudana a New Zealand da Australia.
Tawagar Three Lionesses ta fatattako Super Falcons ne bayan da ta doke ta ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a yau Litinin.
- Matan Kano da aka taba canza sunayensu a jerin ministoci
- An sace Sarki da matarsa a cikin fada a Nasarawa
Wannan ya biyo bayan canjaras ne wanda babu ci da bangarori biyun suka yi a wannan safiya ta Litinin, a wasan da ya bai wa masoya kwallon kafa nishadi.
Ingila ta karasa wannan wasa da ‘yan wasa 10 har zuwa matakin karin lokaci, bayan da a minti na 87 alkaliyar wasa ta sallami Lauren James, shahararriyar ‘yar wasansu, wadda ta ci kwallaye 3 a matakin rukuni.
Cikin fushi Lauren ta taka bayan Michelle Alozie wadda ta fadi kasa a minti na 87, bayan kwallo ta kubuce daga kafarta.
Ingila za ta yi karon batta da Jamaica ko kuma Colombia a wasan daf da na kusa da karshe a birnin Sydney, ranar Lahadi.