✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ingila na son yin wasan sada zumunta da Najeriya

Qasar Ingila ta nuna sha’awar yin wasan sada zumunta da Najeriya.  Ingila ta ce tana son yin haka ne kafin a fara Gasar Cin Kofin…

Qasar Ingila ta nuna sha’awar yin wasan sada zumunta da Najeriya.  Ingila ta ce tana son yin haka ne kafin a fara Gasar Cin Kofin duniya a baxi a Rasha.

Kamar yadda wani rahoto ya nuna, qasar ta tuntuvi Hukumar qwallon qafa ta Najeriya (NFF) ne jim kaxan bayan qungiyar Super Eagles ta haye gasar cin kofin duniya bayan ta samu nasara a kan Zambiya da ci 1-0.

Sai dai kamar yadda bayanin ya nuna Ingila ta ce wasan ba zai yiwu ba idan har Hukumar FIFA ta haxa qasashen biyu a rukuni xaya a gasar ta cin kofin duniya.

“Mun samu takardar gayyatar yin wasan sada zumunta daga Ingila kuma Najeriya tana yunqurin ganin hakan ya kasance, sai dai idan aka haxa qasashen biyu a rukuni xaya a gasar cin kofin duniya to wasan ba zai yiwu ba”, inji wani daga cikin jami’i a Hukumar NFF da bai so a ambaci sunansa ba.

Sau biyu qasashen biyu suka tava haxuwa a wasanni biyu watau a wasan sada zumunta da kuma a Gasar Cin Kofin Duniya.  Na farko shi ne wasan sada zumunta a shekarar 1995 inda wasan ya gudana a filin wasa na Wembley kuma Ingila ce ta samu nasara da ci 1-0 sai kuma haxuwar da suka yi a gasar cin kofin duniya da aka yi a Japan/Koriya a shekarar 2002 inda aka tashi wasan babu ci 0-0.