✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC za ta gudanar da karashen zaben Delta ranar Lahadi

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) reshen Jihar Delta ta ce za ta gudanar da karashen zabe a kananan hukumomi biyu na jihar. Baturen zaben jihar,…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) reshen Jihar Delta ta ce za ta gudanar da karashen zabe a kananan hukumomi biyu na jihar.

Baturen zaben jihar, Dokta Monday Tom, ya ce za a gudanar da zaben ne ranar Lahadi a kananan hukumomin Ukwani da Warri ta Kudu.

Ya bayyana cewa za a yi zaben ne saboda rashin kai kayyyakin zabe masu muhimmanci da hukumar ba ta yi ba a ranar Asabar.