’Yar takarar Gwamnan Jihar Adamawa karkashin jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta dauka na bayyana zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba.
Yayin da ta bayyana a cikin shirin Politics Today na gidan talbijin din Channels Tv, Sanata Aishatu Binani ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu kananan hukumomin jihar.
- Zanga-zanga ta juye zuwa rikici mafi muni a zamanin Macron
- Dalilin da Tinubu ya tafi ziyara kasashe uku
Sanata Aishatu ta ce “matsayina game da matakin shi ne jami’in tattara sakamakon zaben jihar ya yi daidai da ya bayyana sakamakon zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba.”
Babban jami’in tattara sakamakon zaben jihar, Farfesa Muhammadu Mele na Jami’ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.
Gwamnan jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa’adi na biyu karkashin jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam’iyyar APC ke da yawan kuri’u 390,275.
Jami’in zaben ya bayyana cewa ba a gudanar da zaben a rumfunan zabe 69 a fadin jihar ba, kuma adadin katunan zaben da aka karba a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar kuri’u 31,249 da ke tsakanin ’yan takarar biyu.