✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta sanya lokacin fidda jadawalin zaben 2023

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta tsayar da ranar Asabar, 18 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za a gudanar…

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta tsayar da ranar Asabar, 18 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da babban zaben kasa na shekarar 2023.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan ranar Laraba yayin taron yini guda na sauraron dokar laifukan zabe ta 2021.

A yayin taron wanda kwamitin Majalisar Dattawa mai lura da sha’anin hukumar INEC ya shirya karkashin jagoranci Sanata Abubakar Kyari, Farfesa Yakubu ya ce suna fatan tsara jadawalin babban zaben da zarar an kammala zaben gwamnan jihar Anambra wanda za a gudanar a ranar 6 ga watan Nuwamban bana.

A cewarsa, hukumar a kan gwiwa take wajen sanin tanadin doka da za ta yi amfani da shi wajen fidda duk wasu tsare-tsare na babban zaben.

A dalilin haka yake kira ga majalisar da ta hanzarta aikin yi wa dokar zabe kwaskwarima da ke gabanta.

“Bisa tanadin dokar da aka kafa hukumar INEC, zaben 2023 zai kasance ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, wanda ya rage saura shekara daya da wata tara da mako biyu da kwana shida daga yau.

“Sai dai muna bukatar samun tabbaci game da tsarin dokokin zaben kafin mu fidda jadawalin gudanarsa.

“Muna fatan cewa Majalisar Tarayya za ta duk wata mai yiwuwa wajen ganin ta kammala ayyukanta wajen yi wa dokar zaben kwaskwarima a kan kari, inji shugaban hukumar.