✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta ba da tabbacin yin sahihin zabe a Edo

Hukumar Zaben ta Kasa (INEC) ta ba da tabbacin gudanar da sahihin zabe kuma karbabbe a zaben Gwamnan Jihar Edo na ranar Asabar. Kwamishin Zabe…

Hukumar Zaben ta Kasa (INEC) ta ba da tabbacin gudanar da sahihin zabe kuma karbabbe a zaben Gwamnan Jihar Edo na ranar Asabar.

Kwamishin Zabe da Lura da Jam’iyyu na INEC, Farfesa Antonia Okoosi-Simbine ta bayar da tabbacin a lokacin da shugabannin jam’iyyar PDP suka ziyarci hedikwatar hukumar a Abuja domin gabatar da takardar matsayinsu a game da zaben.

Ya ce, “Hukumar na sane da fargabarku kuma za mu yi iya kokarinmu wurin gudanar da sahihi kuma karbabben zabe cikin aminci.

Kwamishinan ya tabbatar musu da cewa Hukumar ta fitar da tsare-tsare na zamani domin lura da kayan zabe daga nesa.

“An sanya wa dukkannin motocin nan na’uran da ke nuna inda suke domin tabbatar da inda suka shiga a kwone lokaci”, inji shi.

Ya kuma ce an sanya wurin rattaba hannun Kwamishinan Zaben na Jiba a kan takardar sakamakon zabe, kmara yadda jam’iyyar ta bukata a yi domin yin komai a fili.

Tun da farko, sai da Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya ce babban abin koyi da INEC za ta yi shi ne gudanar da sahihin zabe.