A Jihar su Lasisi
Inda ake samun lasisi
Mutane na ta lallaga sisi
’yan kasuwa na zuwa birnin Kumasi
A tari ba a wasiwasi
Ranar tara taro da sisi
Mu daina yawan daukar bashi
Sana’a mu yi babu fashi
Matasa an sa muku karsashi
Kamfanin inshorar Inda-sisi
Mutane masu hankali
Sun san fa’idar tattali
Da dukiya a daina yin fatali
Don magance matsaloli
Talauci a datse shi da kansakali
Almubazzaranci
dibar kudi da kici-kici
Wani na jiran a ba shi tukwici
Rashin aiki ne babban lalaci
Da kwazon a ke kwatar ’yanci
A Haurubja
An yi ja-in-ja
Jayayya baja-baja
Na-mujiyar wasu yai kwajaja
Miyagu sun yi basaja
Inshora
Ko in yi shawara
Don ba ta maganin asara
Sai dai a samu a sarara
Mai tari shi zai yi kakara
’Yan sakanni-in-dire
Ku yi tari ku murmure
Kada aljihu ya dare
Masu sane na zare-zare
Kar a kyale su su haure
A tare- a tare
Kowa ya tattare
Amma ban da sare-sare
A kafa shinge da kututture
An dana tarko kafin su ketare
A gayauna ba na tsunbure
A kasuwa ake cinikin furfure
Wajen sayen kaya farare
A ba ni kwalbar turare
In dawo in huta a azure
In ka ji fada ya kaure
Har ana ta mare-mare
A daina shure-shure
Matan gida a daina daga tabare
Kada a tabarbare ai bare
’Yan makaranta ai asusu
Maganin masu sace kudin masunta
Kar a koma ana tata
A barbada samandagarin samarin kusu
Don a ji dadin sana’ar su.
A rana ta kofar hanci ga watan Ukun-toton-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da kwanciyar magirbi, kamfanin Inshorar-Inda-sisi ya yi bikin tattalin taro da sisi na duniya, inda ya ziyarci ’yan makaranta a Haurubja, wadanda ke fafutikar a sake su su dire, amma kada su dare, don haka aka nusar da su muhimmanci tara matsabbai, don kada a nunke su a baibai su rasa ’yan kwabbai.
Duk da cewa kamfanin Inda-sisi ya dan tagaza wajen ganin ‘’yan dugwi-dugwi ba su gaza ba, wajen tarairayar tsilli-tsillin matsalolin rayuwa da ke tunkararsu, amma akwai gyara guda da ya kamata a aiwatar matukar ana son inganta harkar tattalin taro da sisi. A duk aikin da mutum ke yi, ya rike shi babu wasiwasi ko da a Jihar su Lasisi, inda ake samun lasisin lallaga sisi, har a samu haurawa zuwa birnin Kumasi. Ina mai tabbacin cewa yadda farfajiyar Dodorido ke fafutikar nusar da al’ummma dabarun tattalin tara taro da sisi ko MAI MARTABA MASANIN SISI-DA-SISI sai ya ce sambarka, musamman ma ganin yadda muke aikin dinke baraka.
Gyaran da nike son yi wa Kamfanin Inda-sisi shi ne a duk sa’adda aka shirya biki ko fadakarwa kan tattali, don gudun kada a tuttule dukiya a tulu, wajibi ne a nusar da al’umma illar da ke tattare da ALMUBAZZARANCI, sannan a sanar da fa’idar da ke tattare da FIFITA MUHIMMAN BUkATU. Bari in doka dan misali:
Taba
Ta tabbata a barta
Amma wasu don tabbbata
Har batta suke yi mata
Su yi kayan mota ya zuwa dambatta
Wannan babu tababa
Hantsi ba hatsi hatsari
In ba ai sa’a ba, sai a fada cikin garari
kuncin rayuwa yai wa al’umma sasari
Fatara tai kamari
Sai an sare bishiyar talauci da gatari
Kafin ’ya’yanta su fara kumburi
Hayakin buki da zamalo da caku basir da sauran nau’ukan tushen bidi’a in ba ka sha ka kunna ka rike duk suna haifar da laulayin jiki da jikkata aljihu. Don haka sai a kiyaye tun kafin su yi mana kaye. Shi kuwa bangaren abin da ya shafi hadarin da ke tattare da rashin farde garka da gayauna don tara nau’ukan hatsi, hakika yakan zama sanadin hautsinewa da TABAHUWA, wadda ba ta afuwa, sai dai tunbi ya yi ta TSUWWA.
Mu ma daliban wannnan makaranta muna taya kamfanin Indasisi da ke hankoron shank an asarar asusun ajiyar Haurobiyawa, tare da zaburar da al’umma muhimmmancin tatttalin tara taro da sisi, murnar ranar tattalin ’yan matsabbai ta duniya. A sha bikin lumui sumul kalau.