✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina yin kida da waka ne don nishadantarwa – Mista Tee

Wani mawaki sannan kuma fitaccen makadin wakoki na zamani wanda ya shahara a kudancin Kaduna Titus Christopher (Mista Tee) ya bayyana cewa kida da waka…

Wani mawaki sannan kuma fitaccen makadin wakoki na zamani wanda ya shahara a kudancin Kaduna Titus Christopher (Mista Tee) ya bayyana cewa kida da waka a jininsa suke kuma yana yinsu ne don nishadi.

Mista Tee, mamallakin dakin hada wakoki (Studio) mai suna Soft Torch Records, ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da Aminiya a dakin hada wakoki na Almuntazar Sound Studio da ke Kafanchan inda ake kiransa domin hada kida, daukar murya da tacewa.

Mista Tee, wanda dan asalin Jihar Filato ne amma haifaffen Jihar Kaduna, ya bayyana cewa baya ga nishadi, ya kan yi wakoki ne don debe kewa ga wadanda suke cikin wata damuwa da kuma isar da sakonni.

“Na fara koyon kida kafin fara waka. A shekarar 2004 ne tafi koyon kida inda na fara tun daga lokacin har zuwa yanzu. Na fara ne da kade-kaden wakokin turanci amma haduwa ta da wani mawakin finafinan Hausa sai ya janyo ni studiyo dinsa a Kafanchan inda na fara kidan wakokin hausa, har na samu kwarewa a kai ta yadda a yanzu in ka ji wakokin Hausa bila adadin da na yi wa kida ba za ka iya bambance su da wadanda Hausawan suka buga ba.

“Ina yin wakoki ne cikin harshen Hausa saboda a nan Arewa shi ne kadai harshen da za ka yi amfani da shi ka isar da sakonka kai tsaye zuwa ga al’umma. Sai dai duk lokacin da na tashi yin faifan bidiyo to na kan sa fassara da turanci saboda ‘yan kalilan da ba sa gane Hausa sosai su gane sakon.

“A bangaren waka kuwa na fara fitar da album di na na farko ne a shekarar 2007 mai suna ‘Abin da ka Shuka’ (Wakoki takwas) na biyun kuma mai suna ‘Bautan Ido’ (Wakoki takwas) na yi shi ne a shekarar 2011. Dukkansu wakoki ne na fadakarwa na addinin kirista. Ka san a addinin kirista muna da hanyar bautan Ubangiji ta hanyar wakoki to ni sha’awata da waka ta sa na dauki wannan hanayar don isar da sakonni. Babban jigon wakokina shi ne isar da sakon zaman lafiya,” Inji shi.

Mawakin ya kara da cewa suna taimakawa kananan mawaka marasa karfi ta hanyar daukar nauyin shirya musu album na wakokinsu a kan kudi kalilan bayan an gama an sayar sai azo a biya su sauran kudinsu inda ya ce suna haka ne don karfafa matasa masu baiwar waka amma kuma rashin kudi ya hana su bayyanar da baiwarsu.