✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina roƙon ’yan Najeriya kada su yi zanga-zanga — Tinubu

An shirya gudanar da zanga-zangar daga ranar 1 ga watan Agusta.

Shugaba Bola Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su dakatar da zanga-zangar da suka shirya yi a watan Agusta. 

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce Tinubu yana son masu shirya zanga-zangar su jira martanin gwamnati game da damuwarsu.

Zanga-zangar da ake gangaminta a Intanet, an shirya yinta ne a watan Agusta kuma za a yi ta ne a duk jihohin Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja.

Ya zuwa yanzu ba a san waɗanda ke shirya zanga-zangar ba.

’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar kayan abinci da kayan masarufi saboda matsalolin tattalin arziki sakamakon cire tallafin man fetur da sauye-sauye ga manufofin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da gwamnatin Tinubu ta yi.

Gwamnatin ta hannun hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da majalisar wakilai, sun yi gargaɗi game da zanga-zangar.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) da Sanata Ali Ndume sun buƙaci shugaban ƙasa da ya magance matsalolin da matasa suka gabatar.

Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya yi gargaɗin cewa zanga-zangar na iya rikiɗewa zuwa tashin hankali da kuma yin ɓarna kamar yadda aka yi a zanga-zangar EndSARS a watan Oktoban 2020, lamarin da ya kai ga asarar dukiya mai tarin yawa.