✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina nan da raina- Matashin da yasha kwata don murnar zaben Buhari

Matashi mai suna Aliyu Mohammed Sani, wanda ake ta yada rahoton cewa, ya rasu bayan ya yi wanka da shan ruwan kwata a Bauchi da…

Matashi mai suna Aliyu Mohammed Sani, wanda ake ta yada rahoton cewa, ya rasu bayan ya yi wanka da shan ruwan kwata a Bauchi da nufin murnar taya shugaba Buhari lashe zaben takarar shugaban Najeriya da aka yi ranar 23 ga Fabrairu 2019, ya ce yana cikin koshin lafiya da ransa.

Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da ya yi da wakilinmu ta wayar sadarwa a yau Laraba. Ya musanta rahoton da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta cewa, bayan yasha ruwan kwata don taya Buhari murnar lashe zabe ya mutu.

Aliyu, ya kara da cewa wasu rahotannin na bayyana cewa, ya rasu ne bayan an kai shi asibiti duk wannan ba gaskiya bane.