✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina nan a APC – Gwamna Amosun

Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa zai fice daga Jam’iyyar APC, sakamakon rashin adalcin da yake zargi an …

Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa zai fice daga Jam’iyyar APC, sakamakon rashin adalcin da yake zargi an  yi masa a zaben fid da gwanin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a jihar.

A wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Otunba Dayo Adeneye ya sanya wa hannu, Gwamnan ya bayyana cewa  hakika akwai matsin lamba da ake ta yi wa Gwamna Amosun na ya sauya sheka, bayan zaben fid da gwanin, sai dai Gwamnan ya ce yana nan  daram tare da Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC.

Tun bayan da Jam’iyyar APC ta bayyana Dokta Dapo Abiodun a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyar APC maimakon Abdul-Kabir Adekunle Akinlade, wanda Gwamnan ke mara wa baya ake ta cece-kuce tare da yada jita-jitar cewa Gwamnan ka iya ficewa daga APC. Sai dai Gwamna Amosun ya karyata haka, ya ce yana nan tare da Shugaba Buhari.

Gwamna Amosun dai ya rasa samun goyon baya ga wanda ya tsayar a takarar fid da gwanin da kuma rasa kujerar Sanata da ya so ya tsaya, bayan ya kammala zangon mulkinsa na shekara takwas.