Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga ci gaban amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.
- Karin bayani kan maganar fyade a gidan aure!
- Najeriya A Yau: Dalilan da ke jawo hauhawar farashin kayan masarufi
Tambaya: Ni na kasance ina neman bukata a gun mijina, amma sai ya hana ya ki ba ni ba tare da wani dalili ba, kawai hakanan don ya muzguna min.
Amma shi in ya bukace ni ina sallama masa, face in ya fusata ni da yawa sai in ce kai ma ka dandani irin halin da kake saka ni.
To na ji kin jero Hadisai masu firgitarwa kan matan da suke wa mazansu kiyo ba tare da wani dalili ba. Tambaya ta shin in miji ne yake cutar da matarsa shi ma zai sami wannan sakamakon?
Amsa: Wadannan Hadisai mata kadai suka ambata ba su ambaci maza ba, wannan kuwa saboda a dabi’a maza sun fi mata yawan sha’awa da yawan bukatuwarta.
Haka kuma a dabi’ance mata su kan yi ramuwar gayya ta hanyar hana wani abu da suka saba bayarwa.
Amma wannan ba shi ke nufin in Maigida ya yi haka bai da wani laifi ba, domin wannan zalunci ne wanda kuma babban alkaba’i ne kuma in ba ta yafe masa ba Allah zai bi mata hakkinta tun daga duniya har lahira.
Kila sakamakon hakan a lahira ya fi na wanda shari’a ta bayyanar game da kiyon mace domin shi Allah mai yin abin da Ya so ne.
Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana cewa mata suna da kwatankwacin hakki daga mazajensu sai dai su mazan suna da karin daraja a kan hakkinsu a kan mata. (Suratul Bakarah, Aya 228)
Ina mazantakar take?
Wannan nasiha ce ga mazan da matansu suka fi su bukatuwa da sha’awa, sannan don zalunci sai su share su har sai ranar da su suka bukace su alhali suna sane da halin da suke ciki na tsananin bukatuwar sha’awa, su sani wannan ba jarumta ba ce, rauni ne!
Ya ku irin wadannan Magidanta, ku sani, babban jigon da aka gina aure a kai, shi ne saduwar ibadar aure don biyan bukatar sha’awar juna, don haka in mace ta zam ba ta iya gamsar da mijinta ko namiji ya zam ba ya iya gamsar da matarsa, to wannan kwakkwaran dalili ne na a raba auren don ta sami wani wanda zai iya gamsar da ita.
Cikar mazantakar da namiji shi ne ya kasance mai gamsar da iyalansa ta kowane irin fanni na rayuwarsu musamman ma ta fannin ibadar aure.
Ku sani, ran dan-Adam na iya daure wa dukkanin bukatuwar rayuwar duniya, amma ban da bukatuwar ibadar aure saboda tsananin karfinta da girmanta, to meye amfanin auren naku da suke yi idan ba za ku iya yi masu maganin tsananin bukatuwarsu ta sha’awa ba?
Sai dai su runka kallon kafirai suna zina don su rage zafi? Dubi irin hadarin da kuke tura matayenku a ciki?
In har kuna son su don me ba za ku sadaukar da ko da sau daya ne a kowane wata don warkar masu da tsananin bukatuwarsu ba?
Wannan wane irin zalunci ne a ce ka aje lafiyayyar mace a gidanka, amma sau uku kadai kake waiwayar ta a shekara?
Duk wani kayan jin dadin da za ka tanadar mata na banza ne tunda ga wani abu da tafi so sama da komai, kuma ya kasance kai kadai ne za ka iya ba ta shi, amma ka hana ta!
Kun sani akwai halattattun hanyoyi da dama da za ku biya wa matanku bukatun sha’awarsu ba tare da lallai sai kun yi ibadar auren ba, to in kuwa akwai to ai ya kamata a yi wannan sadaukarwar.
Ku tuna in ku ne kuke cikin hali irin wanda matanku suke ciki, za ku so a yi muku haka?
A ji tsoron Allah dai! Mazantaka ba a kira ko siffa ko halitta take ba, mazantaka a kwakwalwa take, don haka in kuna tunanin ku cikakkun mazaje ne ta kowane fannin to haka za ku kasance.
In kuma kuna tunanin kun cika mazaje ne ta fannin biya wa matanku bukatun masarufi kadai amma ban da bukatunsu na sha’awa to hakan za ku kasance.
Kuma Ibadar aure ba biyan bukatar sha’awa ne kadai ribarta ba, tana sanya rahama da tausayi tsakanin ma’aurata, kamar yadda Ayoyin Alkur’ani mai Girma suka yi bayani.
Sai mako na gaba insha Allah. Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin.