✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ina kudin baje-kolin Hauro?

Haurobiyawa na cike da mamakin batan dabon da aka ce kundin baje-kolin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama ya…

Haurobiyawa na cike da mamakin batan dabon da aka ce kundin baje-kolin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama ya yi, har ta kai ga a teburin mai shayi ana ta ce ce ku ce. Tambayar dai da wani ya bijiro mini da ita a safiyar ranar sili da kofar hanci na watan janye-wurin shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, it ace Ina kundin baje-kolin Hauron Haurobiyawa, wanda Baban-burin-huriyya ya gabatar wa majalisar kasa? Ni kuwa na ce masa na hango Saurayin-kirinki sun garkame kofa da shugaban kasa; ko me suka tattauna, ban sani ba.
Ina cikin tattaki zuwa wajen kwadagon neman kadago, tun agogo bai gama wulwulawa ba, sai na fasko cewa, akwai bukatar a lalubo wa masu shan shayi amsar su. Domin kada su je, su yi ta shaci fadi. Ni dai ba ni da masaniya, ba kuma kala wa Dogarin wakilan rafkiya ba, ko kuma Saurayin Kirinki na Majalisar Tsofaffin Haurobiya, wai in ce su suka arce da kundin, a’a!
Batu na kwangiri karfen jirgi kundi na nan inda aka boye shi. Ana yada jita-jitar batan dabon sa ne kawai domin a sanya wa Haurobiyawa hawan jinni, musamman ganin mun shigo watan Janye-wuri, har m,una yunkurin gangarawa cikin Farin-biri; kun ga ke idan an shiga cikin wtan Marisa sai a yi mana mursisi. Ta da fada cikin wta A-farin-lilo, mahukunta su ce mana tsuntsu ne ya wafce kundin ya tashi da shi “Fur!”
A wata mai sunan “Mayu” kuwa, tabbas suna iya ce muku “mayu” sun lashe kundi. Kai ina tabatar muku da zarar an fada cikin wata Yuni, sai su yi ta yawon wuni-wuno da ku. Ta yiwu su bari a kai watan Yawon-wulli, don su wulwula kwanyar ku. Idanj kuwa aka shiga watan ruwa, sai su ce ku ci gaba da kwankwadar na-kwadi. Da an shiga Satin-Baba, sai su ce ku daga sauti har Baba ya ji.
Al’ummar Haurobiya, miyagun da suka wafce wannan kundi suka arce da shi, suna iya yin likimo har sai an kai watan Ukkun-Baba, su ce muku, komai ya balbace, ya damalmale. Don haka kun shiga kofar hancin Baba kun kudundune. Dazarar kun yi sakaci da sakarci, har wannan bada1kala ta kai cikin watan Noman-Baba, sai a umarce ku, da ku fantsama cikin gayauna, inda za ku yi sana’ar na-duke da limbu-limbu a cikin lambu. Da an kamala noman-Baba., sai a ingiza keyar ku wajen Dashen-Baba.
’Yan makaranta, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da mujallu da mukalu da jaridu a farfajiyar Dodorido da ke amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, wasannin ’yan dugwi-dugwi ake son yi da kwanyarku. Ko kuma ta yiwu so suke yi Baba ya ce a kirawo uwargida Lagad, tsohuwar minister kasafin Hauro ta kasar Faransa, wadda a halin yanzu take jagorancin Hukumar Hanjin-ligidin Lamunin Duniya, don ta tsakuro mana wasu ’yan matsabbai daga Langar Ligidinta. Domin akwai wadanda bas u dadi ba, cewa Haurobiya bat a bukatar bashi daga wannan tsohuwa. Kai ko mu da muka sha hanjin ligidin da muka rika saye a wajen Iya, ai ba ma bukatar wannan lamuni na Ladidi da Lamunde.
A wurin miyagu dai, uwargida ta kawo Langar lagwada ne, don su kwashi gararumar gyaran jar-miya. Ni kuwanasan hanjin ligidi ta kawo, shi yasa ma Baban mu ya ki saye. A wannan karon dai masu kwasar gararuma ba su wanye lumuyi ba, tunda sanin kowa ne ana fama da badakalar wawurar kudin makaman artabu da Kanari Samun Bom Da-sauki ya yi, inda ya yi ta jinka wa Haurobiyawa manya da kanana.
Abin da kawai nike son nusar da mu, shi ne, a wannan karo samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya ba za su shad a dadi ba. Domin Baba ya umarci Iro Mugun madambaci ya danko duk wani mugu mai magu-magu. Kai a rana ta sili da karamin lauje ga watan Janye-wuri na ga labarin shugaban Hukumar Kwakwazo ta Haurobiya, a gaban jaridar Dalilin-taron su, kai kusan daukacin manyan jaridun Haurobiya sun baje shi a shafukan gaba, inda aka ruwaito cewa, ya bude asusun sirri makare da Hauro gashin balama sili da kwanciyar magirbi. Haurobiyawa berayen suna da yawa. Don haka har sai kun gaji da jin labarin su.
Wadannan al’amura da suka wakana a Haurobiya, sun tabbatar mana da cewa, tsawon shekaru sili da manuniyar sama da jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta yi,  tana jan ragama, babu abin da ta tafka illa ta’asa a kwanon tasa. Hasalima ga Akuyar-maman-Daudu can tana fuskantar shari’a saboda yunkurinta na yin jabun kundin dokokin majalisa, don kawai a rika bin soye-soyen zukatan su. Ni dama tuni na gaya muku cewa, ai ’yar iska, ’yar iska ce, na kuma dawo na bayyana muku cewa, ita Jakadiyar sheke aya ce.
Tarin miyagu dai na nan da ba su son ganin an aiwatar da aikace-aikacen da aka zayyana cikin kundin baje-kolin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama. Lallai mu nemi tsari daga sharrin su. Ko suna so, ko bas a so, da yardarm Mai-duka sai an zubo mana damin Hauro tiren-taliya manuniyar sama.