✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina goyon bayan El-Rufa’i kan korar malamai – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayan yunkurin sallamar malamai kimanin 22,000 wadanda suka fadi jarrabawar da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi musu. Shugaban kasar…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayan yunkurin sallamar malamai kimanin 22,000 wadanda suka fadi jarrabawar da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi musu.

Shugaban kasar ya ce ba zai yiwu a ce malamin da ya kasa cin jarrabawar dalibinsa ba, ya ci gaba da koyar da dalibin.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da yake jawabi a wani babban taro kan ilimi wanda aka gudanar a Abuja.

A watan jiya ne gwamnatin Jihar Kaduna ta yi wa ’malamai dubu 33, jarrabawa irin ta yan aji hudu na firamare, amma kamar yadda gwamnati ta ce, kashi biyu bisa uku na malaman ba su samu kashi 75 cikin 100 ba, bayan da sakamakon jarrabawar ya fito.

Shugaba Buhari ya ba da labarin yadda ya yi karatu a lokacin da yake maraya, inda ya ce: “Na kasance maraya lokacin da nake yaro, har yanzu na yi amannar cewa duk abin da na yi a rayuwa ya ginu ne daga rayuwata a makarantar kwana. Na yi shekara tara a makarantar kwana, shekara uku a firamare, shida a sakandare.”

Ya ci gaba da cewa: “A wadancan shekarun, malamai suna daukar dalibansu tamkar ’ya’yansu. Idan ka yi daidai za su fada maka, idan ka yi ba daidai ba kuma za ka sha duka.”

Shugaba Buhari ya ce bayan da ya kammala makaranta da gangan ya ki yin aikin gwamnati, ya shiga aikin soja. “Na taba jin wani dan Najeriya wanda nake girmamawa, ya ce bayan ya samu horo a Najeriya da kuma Amurka, ya koma makarantar firamare don ya ba da gudunmawa. Amma sai ya kasa bambancewa tsakanin dalibai yara da kuma malamai.

“Abin da El-Rufa’i yake kokarin yi a yanzu, daidai yake da abin da wancan mutumin ya fada min shekara 10 da ta gabata. Ba zai yiwu a ce malamin da ya kasa cin jarrabawar dalibinsa ya ci gaba da koyar da dalibin ba. “

Yunkurin sallamar malaman da Gwamna El-Rufa’i ke yi yana ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, inda wadansu ke goyon bayan hakan, wadansu kuma ke ganin bai dace a raba mutane da hanyar samun abincinsu ba.