✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina gaskiyar ikirarin Gwamnatin Tarayya na samar da ayyukan yi?

A kwanan nan ne Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa kansa kirari, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta farko da ta samu nasarar samar…

A kwanan nan ne Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa kansa kirari, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta farko da ta samu nasarar samar da guraben ayyuka 5,400 na kai tsaye ga matasa. Ya ce sun samu wannan nasara ce ta hanyar shirin samar wa matasa ayyyuka da sana’o’i (YouWin). Ya gabatar da bayanin ne a yayin da yake maimaita kaddamar da shirin a gidan gwamnati da ke Abuja.

Da yake karin haske game da shirin, shugaban ya ce ’yan kasuwa 2,500 da suka tallafa ma wa, su kuma kowannensu ya tallafa wa akalla matasa tara kowannensu da sana’a ko aikin yi, wanda haka ya samar da jimillar guraben aiki ko sana’a ga matasa 22,000. Ya kara da cewa, ’yan kasuwa su ne kashin bayan bunkasar tattalin arzikin kasar nan, inda suka dauki kashi 60 cikin 100 na wadanda ke samar da kudin shiga na kasa, wanda ya kai adadin jimillar dala biliyan 510, a yayin da su kuma kanana da matsakaitan ’yan kasuwa suka samar da kashi 98 na guraben ayyukan yi a kasar nan a kowace shekara.
Ya ce wannan shiri nasa, ya samu nasara mai yawa, musamman ma ganin cewa ya gaza ne kawai da kashi 10 cikin 100 wajen samar samar da guraben aiki ga matasa. Ya ce wannan nasara mai yawa ce kuma ta kasance ta ba-zata. Ya ce gwamnatinsu ta ankara da cewa rashin aikin yi ga matasa shi ne babban kalubale da ya kamata a tunkara domin magance shi. Kamar yadda ya ce, wannan ne dalilin da ya sanya gwamnatinsa ta dauki himma wajen magance shi. A lokacin da ya fito da shirin, Shugaba Jonathan ya ce ya kudurci samar da guraben aikin yin da ba za su gaza miliyan biyu ba kowace shekara.
Abin lura a nan kuma shi ne, idan dai har guraben aikin yi miliyan biyu aka kudurci samarwa a duk shekara, to ke nan daga bayanin nan na sama, shugaban ya karyata kansa da kansa ke nan kuma ya shafa wa kansa bakin fenti, cewa ya gaza. Domin kuwa a tsawon shekara shida da kafuwar gwamnatin nan, ya akamata a ce ta samar da guraben aiki miliyan 12, amma sai ga shi shugaban da kansa yake nuna cewa gurabe 5,400 kawai ya samar a wannan kididdiga kuma yana cewa ya samu nasara. Daga yadda wannan kididdiga ta nuna, ke nan wasu gwamnonin jihohin ma sun fi Gwamnatin Tarayya samun nasara ta wannan fanni. Misali, Kwamishinan Al’amuran Kasuwanci na Jihar Ogun, Bimbo Ashiru ya bayyana cewa gwamnatin jiharsu ta samar da guraben aikin yi 100,000 ta hanyar raba basussuka ta Bankin Raya Masana’antu tsakanin Nuwamba 2011 zuwa Disamba 2014.
Haka kuma, hatta adadin gurabe 5,400 da ya ce ya samar, akwai tababa a cikinsu, domin kuwa a kwanakin baya, Ministar Al’amuran Kudi, Misis Ngozi Okonjo-Iweala ta yi ikirarin cewa gwamnatinsu a 2013 ta samar da guraben aikin yi miliyan daya da dubu dari shida, a shirin da gwamnatin ta kirkiro na Sure-P. Wannan tufka da warwara da sabani da aka samu wajen kididdigar nasarar adadin guraben aiki da aka samar, yana nuna shakku a ciki, kuma haka ke nuna irin yadda gwamnatin ke wa batun magance rashin aikin yi rikon sakainar kashi.
Gwamnatin ta gaza wajen samar da isassun guraben aikin yi, musamman saboda ta ki fadada al’amarin zuwa bunkasa harkokin noma da kiwo, sai ta fi mayar da hankali wajen samar da ayyukan zamani, wato na gwamnati ko na kamfanoni.
daya daga cikin abubuwan da ke kawo wa tattalin azrkin kasar nan barazana shi ne batun rashin aikin yi da ya yi kamari ga matasa, musamman ma wadanda suka gama karatu a matakan ilimi daban-daban. Kamar yadda bayani ya tabbatar, Najeriya ce ke kan gaba cikin kasashe masu tasowa inda rashin aikin yi ya yi wa matasa katutu. Irin yadda aka samu turmutsitsin matasa da suka nemi shiga aikin Hukumar Shige-Da-Fici a 2014, wanda har ya haddasa mutuwar wasu daga cikinsu, hakan na nuna irin yadda rashin aikin yi ya yi kamari a kasar nan. An kiyasta cewa a duk shekara, ana samun matasa miliyan biyu, wadanda suka gama jami’a kuma suke neman aikin yi.
Babu shakka rashin aikin yi ba karamar illa yake haifarwa ba ga al’umma, don haka ya dace gwamnati ta mike tsaye wajen nemo hanyoyin magance shi. Za a iya rage matsalar ko magance ta ta hanyar samar da kananan da manyan masana’antu, da bunkasa noma da kuma samar da ingantattar wutar lantarki.