✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina da yakinin cin zabe — Binani

Duk da ban san ilimin gaibu ba, amma ina kyautata zaton zan yi nasara.

’Yar takarar gwamnan Adamawa a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani ta ce tana da yakinin lashe zabe a jihar.

Sanata Binani ta bayyana hakan ne bayan ta kada kuri’arta a rumfar Mbamoi mai lamba 006 da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu.

Ta ce ba ta san mai zai wakana ba saboda babu wanda ke da ilimin gaibu, amma tana da yakinin cewa za ta yi nasara.

Ta gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da kuma al’ummar Adamawa mata da maza da irin goyon baya da suke bata.

%d bloggers like this: