Babban malamin nan na addinin Islama kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), ya bayyana cewa yana da shakku a kan ingancin rigakafin cutar Coronavirus da ake neman kawowa kasar nan.
A wata hira da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi tare da manema labarai ranar Asabar a birnin Jos, ya ce har yanzu bai aminta da ingancin rigakafin ba amma hakan ba ya nufin kira ne a kan kada mutane su karbe ta.
- Mutum 994 ne suka rasu a hadura a Abuja a 2020 —FRSC
- Najeriya za ta yi dokar hukunta masu tsangwamar mata masu Hijabi
- Harin Boko Haram kan turakun lantarki ya jefa Maiduguri cikin duhu
Ya ce, “Har yanzu ban gamsu da rigakafin ba amma duk wanda ya aminta da sahihancinta yana iya karba.”
Sheikh Jingir ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta Jihohi a kan kada su yi gaggawar yanke shawarar yi wa ’yan Najeriya rigakafin ko kuma tilasta su a kan karbarta.
Ya ce ’yan Najeriya da dama ciki har da masana kiwon lafiya da wasu jami’an gwamnati na da shakku a kan rigakafin, lamarin da ya ce rayuwar mutane na da muhimmanci wanda a dole sai an yi taka tsan-tsan.
Ya bayar da shawarar cewa kafin a dauki duk wani mataki a kan rigakafin, akwai bukatar gwamnati ta nemi kwararru su gudanar da bincike mai zurfin gaske sannan su fito da cikakken bayani game da sakamakon da suka gano.
Ya ce hakan ita kadai ce hanyar da za ta bai wa ’yan Najeriya damar yanke shawarar karba ko juya wa rigakafin baya.
“Tabbas ina da shakku a kan rigakafin amma hakan ba ya nufin kira ne ga sauran mutane su juya mata baya domin kuwa zabi ya rage ga kowane mutum dangane da gamsuwa ko sabanin haka.”
“Duk wanda ya gamsu da igancinta, yana iya karba amma shawarata ita ce gwamnati ta yi bincike mai zurfin gaske a kan rigakafin gabanin sahalewa mutane su karba,” inji Sheikh Jingir.
A watan Janairun da ya gabata ne aka sanar da cewa za a yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo rigakafin cutar a bainar jama’a wanda gidajen talibin za su yada domin kara wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwar amincewa da ita.