✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina cikin jerin masu karuwa da Aminiya

Salam. Editan Aminiya mai frin jini.Hakika muna jin dadin karanta jaridar Aminiya, kuma muna jin dadin watsa ra’ayin masu karatu, domin kuwa muna karuwa da…

Salam. Editan Aminiya mai frin jini.Hakika muna jin dadin karanta jaridar Aminiya, kuma muna jin dadin watsa ra’ayin masu karatu, domin kuwa muna karuwa da abin da ake bayyana wa wannan, musamman abin da ya shafi ra’ayoyin jama’a da addini da siyasa da zamantakewa.
Anan nake cewa don Allah ku sani cikin masu karanta Aminiya. Allah Ya taimaka ya sa albarka. Allah Ya kara muku kwarin gwiwa.
Daga Amininku  Yahaya Muhammad Maina, Shugaban Kamfanin Sarrfa kayan gwangwan (na Maina Scraps & Fishwery Keeping Company). 08022146489/07037108851

Sakonnin waya

Ga Edita
Assalamu alaikum wai me ya sa ba ku rubuta sakon waya ta ne? Daga dan Funtuwa, Jihar KAtsina 08099522225.

Me Aljannarawa suka yi wa Edita?
Zuwa ga Editan Aminiya, wai me Aljannarawa suka yi wa Edita ne da ba ya buga sakonmu? Shin ko ana ba Edita wani abu ne? Mu ma mu aiko da namu, don ba a fi mu son Aminiya ba. Da fatan Edita zai gyara, mun san Aminiya ta birni da kauye ce. Daga Muhammad dangide Aljannare, Jihar Kebbi 07039681194.

A dawo da Dausyain kauna
Salam zuwa ga Aminiya don Allah ku taimaka ku dawo mana da Dausayi kauna. Daga Sani Lawan Kurna Asabe 08035000177.

Babu adawa a Hadeja da Auyo
kalubale gareku ’yan Majalisar Tarayya na Jihar Jigawa. Muna kara godiya da irin ci gaban da dan majalisarmu ya kawo mana. Hon Hussaini Namadi. Domin a yanzu babu adawa a Hadeja da Auyo da Kafin-Hausa. Muna kara jadadda goyon bayanmu ga jagorarnmu Alhaji (Dokta) Sule Lamido CON. Daga Ahmed Fada 07065550587.

Hattara matan aure
Assalamu alaikum. Allah Ya kara daukaka Aminiya. Ina jan hankalin al’umma da su yi hattara da wasu mata masu shiga gidajen matan aure, musamman in gidan an yi sabuwar amarya, don su kwashe zannuwa. Babu wanda zai iya cewa komai har sai sun fita.domin irin wannan ta faru a wani gari da ake kira Dutsen Abba, a kan hanyar Zariya zuw aKaduna. Daga Maryam AbdurRasheed Jaji, Kaduna 07032366792.
Edita ka ba ni dama in jinjina wa ’yan majalisar Jihar Kaduna saboda mayar da ’yan bigilante karkashin gwamnati. Allah Ya sa sauran gwamnonin arewa su yi koyi, domin tsaro ya inganta a kasa baki daya. Amin. Daga Zubairu Mustapha Saminaka, Jihar Kaduna, Najeriya 08057027244.

Ga kauran Bauchi
Assalamu alaikum. Edita ina son ka ba ni dama a jaridarmu ta Aminiya don mika godiya ta musamman ga Sanata Bla Muhammad kauran Bauchi, saboda gina mana asibiti da ya yi a Goskwaram Bauchi LGA, wato karamin dakin shan magani na  PHC. Allah Ya saka da alherinSa. Amin. Daga Alhaji Sule Goskwaram 08081381721.

Ga Ali kwara
Don Allah Aminiya ki gaya wa Ali kwara ya daina yi wa gwamnati aiki da jami’an tsaronta. Daga Isa Waliyi Zaggi Nahuce, Jihar Zamfara 08026918933.

Almakura ba ka yaudara
Almakur aka bai wa mara daya kunya. Ko da goma ta lalace, ai ta fi biyar. Aikin gwamnatin CPC a Jihar Nasarawa ba karya, ba yaudara. Abin da PDP ta kasa yi ne CPC ta yi. Daga Ibrahim AB Balarabe ZAriya City 08023442901.

Almakura ban da yaudara
Gwamnan Nasarawa, Alhaji Umar Tanko Almakura, mun fara gajiya da mulkin yaudara da kuri’a. Muna bukatar a cika mana alkawarin da aka dauka, amma ba a dinga yi mana yaudara ba. Daga Tanko Yusuf Lafia 07061056408.

Mu zabi Solomon Dalong
Assalamu alaikum. Edita don Allah ka ba ni fili in yi kira ga talakawa ’yan uwana, mu yi hakuri, mu mara wa Solomon Dalong baya zabe mai zuwa 2015, a karkashin jam’iyyar talakawa ta APC. Saboda shi zai yi adalci ba ruwan shi da adinanci ko kabilanci. Daga Nasir bin Idris Keffi, Jihar Nasarawa 07088857916.

Haba jama’ar Taraba!
Don Allah ko akwai wata riba da ake tsunta a tashin hankali? Da fatan Musulmi da Kirista a Jihar Taraba za ku maida wukarku kwabe. Daga Hassan Muhammad Binanchi, Unguwar Magajin Garin Sakkwato. 08050579884.

Ga Hauwa’u Adamu Gombe
Goodluck Shugaba ne mai adalci, dubi irin aikin da ya yi a Baga kwananan nan. Allah Ya ganar da ke. Daga Khadija Alhassan Zariya.

Aurar da zawarawa a Bauchi?
Assalamu alaikum. Ya hada-hada, ya aiki? Ina mika gaisuwa ga ma’abota wannan fili, tare da fatan kowa na cikin koshin lafiya. Don Allah Gwamna Isa Yuguda da gake ne za ka fara aurar da ’yan amta da zawarawa? Yaushe za ka fara; kuma tawa ce hanya za a fara? Akwai ’yan uwa da za a taimake su, ta wannan hanyar. Daga Khadija SH Azare 08061303383.

Kira ga Shugabannin Arewa
Aminiya ’yar amana, don Allah ku mika mana kira ga shugabanninmu na Arewa, a 2015, su ji tsoron Allah su dubi halin da Arewa take ciki na rashin tsaro da talauci. Ku tun maganar Malam Aminu Kano “Najeriya daya ce, amma kowa ya san gidan ubansa. Daga Musa Unguwar Mai Yasin da Taimakon Sumaya 08155648155/08140205244.

Matasa adaina cika baki a aure
Zuwa ga matasan Najeriya, don Allah idan suna neman aure, su daina karyar ciyarwa da shayarwa da tufatarwa. Wannan matsalar ita ce take kawo yawaitar mtasan zawarawa a duniyar auratayya. Daga Ali Fancy Garko A. Kano 08156589750.

Ga Kawu Sumaila
Kawu Sumaila mun ki wayon, an shamu mun warke. Kishin Musulunci ba a baki yake ba; in ka so mu tabbatar kana kishin Musulmi ka koma ka musuluntar da maguzawan Sumaila d aTakai, a Jihar Kano, wannan shi en babban jihadi. Daga Abdulkadir Abba dangoro 08153027115.

Ga Ali kwara
Don Allah Aminiya ki gaya wa Ali kwara ya daina yi w agwamnati aiki akan azalumai, saboda ita kanta azaluma ce, it ad ajami’an tsaronta. Daga Isah Waliyi Zaggi Nahuche, Zamfara.