Wani kwararre a harkar ruwa Mista Matthew Offie ya bukaci ’yan Najeriya da su rika bin ka’ida wajen hakar rijiyoyin burtsatse domin kauce wa tsumburewar kasa da ruftawar gine-gine.
Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Talata cewa abin damuwa ne yadda hakar rijiyoyin burtsatsen ya zama hanya guda da mutane suka dogara wajen samun ruwan amfanin yau da kullum.
Ya kwatanta lamarin da tsamurewar kasa, masanin ya ce hakan na faruwa ne sakamakon yawan hakar ruwan karkashin kasa da ake yi.
“Dalilin hakar rijiyoyin barkatai na da nasaba da yawan bukatar ruwan da ake da shi. Idan mutane ba su da ruwa, to za su koma hakar rijyoyin burtsatsen.
“Yanzu kusan kowa a nan yana da rijiyar burtsatse na kansa.
“Ba a kula da harkar hakar rijiyoyin a yanzu. Don haka muna bukatar dukkanin gwamnatoci da su himmatu wajen samar wa jama’a ababen more rayuwa na yau da kullum musamman ma tsaftataccen ruwan sha.’’
A cewarsa, hakan zai taimaka gaya wajen rage hakar rijiyoyin barkatai musamman da wadanda ba kwararru suke yi hakar su ba, da zai kare albarkatun ruwayen karkashin kasa a Najeriya.
Ya kara da cewa haka rijiyoyin a kusa da salga shi ma abin damuwa ne saboda yana haifar da samar da gurbataccen ruwa wa al’umma.
Ya ce lallai ne tazarar rijiyoyin burtsatsen da salga kada ya gaza mita 60 maimakon yadda ake yi a wasu wuraren inda ake samun tazarar mita 15 tsakaninsu da salga.
A cewarsa, hakan ba abin da za a amince da shi ne ba sakamakon ana iya samun gaurayar ruwayen duka biyu inda za su gurbata juna.
Masanin ya ce ana yawan samun hakar rijiyoyin barkatai a unguwar Lekki da ke birnin Legas, inda ya ce da a ce hukumar ruwa ta Jihar Legas na samar da ruwa yadda ya dace to kuwa da babu bukatar rijiyoyin burtsatsen da dama.
A baya dai Ma’aikatar Kula da Albakatun Ruwa ta Tarayya ta kafa Dokar Kasa kan Haka da Ayyukan Gina Rijiyoyin Burtsatsen.