✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illar fara dindiba: Misalai daga wakokin marigayi Malam Maharazu Barmu Kwasare

Tarihin da taskarmu ke dauke da shi a yau shi ne, tarihin fara dindiba wadda ta yi sanadin hasarar hatsin al’ummar garuruwa da yawa. Farar…

Tarihin da taskarmu ke dauke da shi a yau shi ne, tarihin fara dindiba wadda ta yi sanadin hasarar hatsin al’ummar garuruwa da yawa. Farar matsayin wani bala’i ce da Allah Ya kawo wa al’ummar da wannan abu ya faru gare su. Kafin fara dindiba ta zo akwai fari iri daban-daban sai dai ba su cuci jama’a kamar yadda fara dindiba ta yi ba.

Lokacin da fara dindiba ta zo duk ta lalata sauran farin da ta tarar suka dauki halinta na cutar jama’a sanadiyyar koya musu da fara dindiba ta yi. Dangane da haka, ga abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce:

Farin kwarai ta bi su duk ta nakkasa,

Duk ta gwada musu yaudara ita dindiba.

Ci-tutu ko tutun mutane ba ta ci,

Tutun hatci taka ci gamonsu da dindiba.

Ga aska, laya da ak kamal laya dakwa,

Duk ta yi muni don gamonsu da dindiba.

Fara zulub ita ba ta zulmi ga ’yan Adam,

Yau ga ta zulmu ta kai gamonsu da dindiba.

Kuma guntuwa ta mai da dawa guntuwa,

Ba ko halinta ba ta bi fara dindiba.

Kai! Dubi sankaladun ga dogon samrayi,

kallat hatci shika yi gamonsu da dindiba.

Ta gayyato fari iri da iri duka,

Sun taimake ta tana ta sharri dindiba.

 

Bayan gayyatowar da fara dindiba ta yi ma sauran fari don su taya ta cutar da mutane ta hanyar lalata musu hatsi cikin gonaki, Malam Maharazu ya bayyana cewa ba ta fara da kowane gari ba sai garin Kwasare. Ga abin da ya ce kamar haka:

 

Ta yo cida ga hatcinmu ta bi ta Acida,

Babu murna kowa ba shi murnad dindiba.

 

Za a gano tabbacin farar ta fara da garin Kwasare a cikin layi na farko in da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce “Ta yo cida ga hatcinmu ta bi ta Acida”. A nan, Maharazu na nufin fara dindiba ta fara daga garin Kwasare sannan ta isa Acida ta ci gaba da lalata musu hatsi a cikin gonakinsu. Mai karatu na iya tunanin cewa, dole farar ta fito ne daga wani wuri kafin ta kawo Kwasare. Wannan haka ne amma, ka da a manta cewa, taskar tarihin da ake bayani kanta ita ce dangane da wakokin Malam Maharazu Barmu Kwasare ne na abubuwan da ya fada da bakinsa tare da kattaba su cikin rubutu. Haka kuma, ba za a kara abin da ba a gani cikin wakokinsa ba kuma, ba za a rage abin da aka gani a ki bayyana shi ba. Saboda haka, ko ta fara da wani gari da ba Kwasare ba, abin da ya dame mu shi ne, abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya fada. Haka kuma, duk abin da aka gani cikin wakokin Malam Maharazu Barmu Kwasare babu na karya ko daya domin an shede shi da cewa mai gaskiya ne.

 

Da farar ta baro garin Kwasare bayan ta kare cida ga hatsinsu sai ta isa garin Acida. Daga Acida kuma, sai ta kai hari a garin Wurno. Da zuwanta karkarar garin Wurno ba ta tsaya wata-wata ba sai ta lullube musu hatsi cikin dukkan karkarinnen garin kuma, babu farar da ta kai fara dindiba sharri kamar yadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ambata:

 

Wurno wurin nomansu duk ta lullube,

Guda, ba wata guda mai nata sharri dindiba.

 

Barin garin Wurno ke da wuya ga fara dindiba sai garin Goyonyo ta yada zango. Daga nan sai Gobir da Moriki da Maradun da Zurmi da Kauran Namoda. Duk garin da farar ta isa babu garin da aka yi murna da zuwanta sai Allah tsine. Daga karkarar Kaura sai ta cirata zuwa karkarar garin Tsafe da Gusau da Kwatarkwashi da Bungudu da Dansadau da Maru da Mafara. A duk wuraren da ta isa, ba ta da aiki sai mayar da zangarnun hatsin da ta tarar a cikin gonaki soje. Wannan ya kara tabbatar da cewa, zuwan fara dindiba ba alheri ba ne ga jama’ar gari face hasara. Daga karkarar Mafara sai farar ta isa Bakura da Gandi da Raba da Shuni da Dange da Anka da kuma Tureta. Fara Dindiba ba ta tsaya a nan ba sai da ta kai wa mutanen Bukkuyum hari ga hatsinsu da na Gummi da Kebbe da Tambuwal da Jabo da Dancadi da Kilgori da Yabo da Bodinga da kuma Sifawa. Duk garin da ta sauka cikin karkararsu sai sun yi Allah tsine. Daga garin Sifawa sai ta kara gaba zuwa karkarar Silame da Wamakko da kuma Binji. Bayan duk garuruwan da aka kawo da fara dindiba ta kai hari ga hatsinsu ba ta tsaya nan ba sai da ta isa Dundaye da Tangaza ta tangaje hatsinsu. Haka kuma ta isa Kware inda a karshe ta isa karkarar garin mutanen Sakkwato ta yi musu ba kyau ga gonakinsu. Domin tabbatar da fara dindiba ta zagaye garuruwan da aka fada a sama ga misalin wasu baitoci kamar haka:

 

Ta bukkuce geron mutanen Bukkuyum,

Gummi ta guma musu zamba fara dindiba.

Ta kebe gonakkin mutan wajjen Kebbe,

Duk Tambuwal ba lambuna sai dindiba.

Ta mai da Dogondaji daji ta wuce,

Sanyinna sai yunwa ta sa musu dindiba.

Bodinga ta bude fikafikanta nan,

Sifawa duk sun sha masibat dindiba.

Silame silallan hatci dai tab bari,

Ta wa mazan Wamakko banna dindiba.

Da zuwanta Binji ban ji ta kadanna ba,

Dundaye ta doda su kaye dindiba.

Ta tangaje su kwarai mutanen Tangaza,

Ta zo Kware ta kwari dawa dindiba.

Ta sakkwato geron mutanen Sakkwato,

Balle na kauye su san ragowat dindiba.

 

Allah mai iko! Bayan duk zagayen da fara dindiba ta yi tana cutar da jama’ar garuruwan ta hanyar cinye musu hatsi a cikin ganakinsu, ita ma ta hadu da tata jarrabawa a garin Goronyo inda suka shuka rake a cikin gonakinsu na fadama. Farar ta shiga karkararsu sai ta yi ta yi musu barnar a rake. Da ta fara barnar rake su kuma suka rika kama ta suna gyarawa suna ci. Domin tabbatar da wannan magana ga abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce:

 

Ita ci takai su ci sukai dada an game,

In ta yi barna sai su yo mata dindiba.

 

A wannan lokaci yara da tsofaffin garin suka dukufa ga kamun fara dindiba kamar yadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya fada:

 

Yaransu mata duk da ‘yan tsoffin gari,

Kowa da nashi buhu shina zuba dindiba.

 

Ba cikin buhuhuwa kadai mutanen ke zuba farar ba, suna zuba wa cikin masaki da kwanduna da mangalinne. Dangane da haka, ga abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce:

 

Masaki da Kwando mangala an ciccika,

Layi guda biyu an cika su da dindiba.

Sun dai ci har sun koshi har da sayassuwa,

Sun bar sayen nama da samun dindiba.

 

Dangane da wannan zuwan fara dindiba an sami hasara da kuma dan amfani kadan, ba kamar sauran wurare da suka cutu ba kurum. Da farko kamawa suke yi suna ci kawai. Daga baya sai suka rika sarrafa ta suna sayarwa. Zuwan fara dindiba hukuncin Allah ne kamar yadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ambata:

Ya Allah na roke ka kai muna gafara,

Na san hukunci na tahowar dindiba.

 

Bayan wannan, an kai matsayin da masu kama fara suka mamaye wuraren zaman ’yan koli a cikin kasuwar Goronyo domin kasa fara suna sayarwa. Dangane da haka ga abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce:

 

‘Yan koli sun zaka babu filin shimfida,

Kwaz zo wurinai mace ta kasa dindiba.

 

Zuwan fara dindiba a garin Goronya ya kawo kari ga sana’o’in da ake yi a garin domin bayan wadanda ke akwai an kara samun ta sayar da fara ga masu yi. Wasu kuma, canza sana’a suka yi baki daya. A kan haka ga abin da Malam Maharazu Barmu Kwasare ya ce:

 

Tsoffin da ke kosai da mashe da dakuwa,

Duk sun bari sun kama suyad dindiba.

Jama’ar Goronyo maza da mata ke saye,

Attajirai da talakka ya sai dindiba.

‘Yan fada, ‘yan sarki da bayin nasu duk,

Kwak kai anini sai shi kwaso dindiba.

 

Kafin zuwan fara dindiba ba a taba suyan fara har a sayar ba saboda rashin yawanta. Tare da haka Malam Maharazu Barmu Kwasare ya faki cewa:

 

Nan taf fi fari dama-dama ga duniya,

Don ko abinci ta, ga mai dindiba.

Wani mai gare ta kaman na turkakken bisa,

Ko kwai akwai arba ga bundin dindiba.

Haka kuma, Malam Maharazu Barmu Kwasare ya fadi cewa, fara dindiba na da saukin kamu saboda nauyin da ke gare ta kuma, goye take da juna. Ba ita kadai take tafiya ba, koyaushe tana goye da ‘yar uwarta. A kan haka, ga abin da Maharazu Barmu Kwsare ya ce:

Kuma ba wuyak kamu gare ta ba don ku ji,

Goyayya biu-biu sai a dauka dindiba.

 

Dano Balarabe Bunza. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo, Sakkwato.

[email protected], [email protected]