✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ikrarin cimma manufofin shekara 100: Tsarin Najeriya

Manufar salon Najeriya na bin tafarkin cimma burin Amurkawa, wadda manufa ce ta amfani da kaifion basira a kishin kasa da hadin kai, ta yadda…

Manufar salon Najeriya na bin tafarkin cimma burin Amurkawa, wadda manufa ce ta amfani da kaifion basira a kishin kasa da hadin kai, ta yadda idan aka samu lokaci da kayan aiki daidaikum mutane zai su iya kaiwa ga cimma babban matsayi. Wannan ita ce manufar tsarin bunkasa Najeriya. Tsarin Inganta Najeriya ya kamata ya zama na cusa wa ’yan Najeriya abin da aka so cimmawa dangane da hade sassan Kudanci da Arewaci, tare da birnin Legas da suka dunkule suka zama kasa guda a tsawon shekara 100. Tamkar dai a  ashekara 1914, mun shigo sabuwar shekara, kuma lokaci ya yi da za mu bibiyi dalilan da suka sanya Najeriya ta nuna gazawa, ta yadda za ta ci gaba da bin tafarkin da aka dorata a baya, sannan ta bude sabon babin ci gaba, a matakin daidaiku da daukacin al’umma.
Al’amarin da ya wakana a shekarar 1914 za ta ci gaba da kasancewa abin ce ce ku ce bisa ra’ayoyi mabambanta. Duk da haka kuskure ne a dauka cewa mutanen wannan yanki da ake kira Najeriya bas a hulda da juna kafin hadewa yankunan biyu da suka zama kasa guda. Tarihi ya nuna cewa tun kafin mulkin mallaka, a daruruwan shekaru kaka da kakanni akwai alkar a tsakanin al’ummomin yankin, ta hanyar cinikayya da auratayya da sauran huldodi. Hujjojin da suka tabbatar da mu’amala da juna a tsakanin kabilu na dada kara dankon zumunta har zuwa yau; abin da kawai aka rasa a lokacin shi ne rashin ganin kawunansu a matsayin ’yan Najeriya, wadanda ke yunkurin bunkasa Najeriya, al’amarin da ya fara wakana bayan an hada kasa, sai mutane suka fara siffanta kawunansu a matsayin hakan.
Babban dalilin bikin da murnar hadewar kasa, shi ne bai wa ’yan Najeriya damar fito manufarsu, wadda za tab a su damar haduwa a kan turba guda da kwakkwarar makoma. Don haka Gwamnatin Tarayya ta ga ya dace ta yi gagarumin bikin tarihi a shekarar 2014, ta yadda Najeriya za ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa, su kuma yi yaki don hadin kanta kamar yadda akanyi basasar wata 30, wadda har yanzu ana jin zafin raunin da aka yi wa kasar. Bayan an kammala sai aka fara tunanin gina kasa, tare da kyakkyawar manufar daidaito da tabbatar da adalci a harkokin gwamnati.
Bikin 2014 zai bayar da damar da ba a taba samunta ba, wajen gano sababbin hanyoyi cire wa mutane tsattsauran ra’ayin nuna kiyayya tsare-tsaren zamantakewarmu, tamkar yadda ake gani a halin yanzu. Bincike ya kamata ya ta’allaka kan yadda za a kafa cibiyoyi managarta da za su tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden dokokin da ake amfani da su, don shawo kan kalubalen da ake fuskanta. Sannan akwai buwatr samar da shugabanci nagari, wanda zai gyara kasa, a samu fa’idoji.
Bisa la’akari da abin da aka zayyano, shugabannin siyasa su yi watsi da munanan dabi’unsu da suka saba da su, su sauke nauyin da ya rataya a kansu, ta wajen samar da shugabanci da hangen nesa, wanda zai ta’allaka wajen inganta zamantakewa a tsakanin al’ummomin Najeriya mabambanta, tare da daidait aharkokin siyasa, don samun bunkasar tattalin arziki. Akwai bukatar samar da dimbin kudi, wadanda za a yi amfani da su wajen tafiyar da tsarin dimokuradiyya, don kyautatuwar zamantakewa da bunkasar tattalin arziki sun dogara ne a akan haka.
Idan har manufar karnin farko ita ce, kafa tushe mai inganci ga kasa, don shawo kan kalubalen da ya dabaibayeta, to sai a himmatu wajen biyan bukatun ’yan Najeriya, don samar musu da kayan more jin dadin rayuwa, bisa tafarkin bunkasar tattalina arziki  da walwala, da kishin kasa, inda za a tattara karfi don tafiya a kan tsari managarci.