Barista A’isha Bukar ta karanci fannin shari’a ne a Jamiár Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato kuma ta zama cikakkiyar lauya a 1992. A halin yanzu ita ce Magatakardar Kwalejin Ilimi ta Kwantagora, kuma Shugabar Kungiyar Magatakarda ta Najeriya. ’Yar asalin Jihar Neja ce da aka haife ta a ranar 11 ga Mayu 1967 a garin Kwantagora. Ita ce ta bakwai a cikin ’ya’ya 10 da mahaifanta suka haifa. Shida mata ne yayin da hudu suka kasance maza. Ta tattauna da Aminiya kan tarihinta da abin da ya sanya ba ta ci gaba da aikin lauya ba da irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa:
Neman ilimi:
Na yi karatun firamare ne a makarantar Firamare ta Magajin Rafi da ke Sakkwato daga 1972 zuwa 1979. Daga nan sai na wuce Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Minna. Bayan na kammala sai na wuce Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato inda na yi digiri na farko a bangaren shari’a. A wancan lokaci da yake makarantar shari’a daya ake da ita a nan kasar wato Makarantar Shari’a da ke Bictoria Island a Legas, to a can na rubuta jarrabawar zama cikakkiyar lauya. Na zama cikakkiyar lauya a 1992.
Ayyuka:
Na yi aikin yi wa kasa hidima daga 1992 zuwa 1993 a Jihar Neja. Da farko an tura ni Jihar Kaduna ne kuma a can na samu horo amma daga baya sai na koma Jihar Neja saboda mijina, wanda yake soja ne kuma yana zaune ne a Barikin Soja na Kwantagora. Na yi aikin yi wa kasa hidima (NYSC) a Kwalejin Ilimi (FCE) ta Kwantagora wato inda nake aiki yanzu. Bayan na kammala sai na fara aiki da wani kamfanin lauyoyi wato Mika Anache and Co. Na yi aiki da su na shekara biyu daga bisani na koma FCE, Kwantagora. Na fara ne da mukamin mai ba da shawara ta fuskar shari’a, haka na yi ta ci gaba har na hau kan mukamin magatakarda..
Abin da ya sa na zabi aikin gwamnati maimakon na lauya
Wannan wani hukunci ne da iyayena suka zartar, ba abin da na yi niyya ba ke nan. Mahaifina ba ya son in yi aikin shari’a saboda a cewarsa ba ya son ya ga wadansu mutane suna zartar da hukunci a kan ’yan uwansu mutane. A koyaushe yakan ce “Idan ka hukunta wani a nan duniya, to kai ma za a yi maka hukunci a ranar gobe. Don haka ba zai yiwu in saba wa umarninsa ba, sai kawai na yi abin da yake bukata. A lokacin da nake aikin, kowane lokaci nakan tuna da bacin ransa. Don haka tilas na yi murabus domin in dadada wa mahaifina.
Abin da nake ji a matsayina ta daya daga cikin kalilan din mata magatakarda
Ina jin dadi, duk da yake aiki ne mai wahala amma ina so, shi ya sanya ma na neme shi da kaina. Ina son in cusa da’a ne, domin wanda na gada namiji ne, wanda ba na jin dadin yadda ya tafiyar da harkar ofishin. Ni kuma a matsayina na mace shi ya sanya na kudiri niyyar in yi amfani da kwarewar da na samu a shekarun da na shafe a nan makarantar in yi abin da ya fi haka.
Kalubalen da na fuskanta wajen samun ci gaba
A lokacin da na fara samun daukaka ta samun mukamai abin bai zo da sauki ba. Lokacin da na kai ga mukamin Mataimakiyar Magatakarda, an ki yi mini karin girma saboda wai a ka’idar aiki ni fannin shari’a na karanta ba fannin gudanarwa ba.
Wannan yunkuri ne na dakile ni, amma sai na zauna na yi karatun ta-natsu na yanke shawarar samun shaidar karatu a fannin aikin gudanarwa. Sai na fara binciken makaratun da suka fi kowanne ta fannin nazarin gudanarwa a Najeriya.
A kan haka ne na tafi Makarantar Koyon Harkokin Shugabanci ta Najeriya(ASCON) da ke Badagry a Jihar Legas na yi babbar Diploma a fannin gudanarwa. Da yake karatu ne da ake yi cikin wata tara, tilas sai na dauki hutun aiki, inda na koma Legas da zama. Da na karbi takardar shaidar kammalawa, sai aka kara mini girma. Kusan shekara biyu kuma bayan haka sai aka shelanta neman masu son mukamin Magatakarda. Take na shiga cikin masu nema.
Da yake mukami ne kamar na siyasa. Kafin in nema, sai da na yanke shawarar cewa a matsayina na mace, mai iyali wannan ba zai taba hana ni cimma wannan buri ba. Sai ma dai ya kara mini kaimin kaiwa ga wannan mukami.
Kalubalen da nake fuskanta a matsayin Shugabar Kungiyar Magatakarda ta Najeriya
Akwai kalubale da dama. Ba abu ne mai sauki ba, abu ne mai wahala. Kafin in zama shugaba sai da na rike mukamin sakatare, yanzu a matsayin shugaba kuma wannan abu ne mai jan lokaci da kuma wahala. Amma dai kin san sa-kai ya fi bauta ciwo, duk abin da ka sanya kanka to komai zai zo da sauki. Don haka ina jin dadin yadda na rungumi wannan mukami.
Yadda nake kula da iyalai duk da dimbin aikin da ke kaina
Duk wannan ya rataya ne ta fuskar yadda ka tsara lokacinka. Idan ka nakalci lokacinka, to za ka tafiyar da haka. Idan aka zo maganar iyali ina bakin kokarina haka idan aka zo maganar aiki ina yin bakin kokarina. Ba na yarda wani ya hana ni aiwatar da wani. Lokacin dawainiyar iyali abin da zan yi ke nan, haka lokacin aiki, aikin ne kawai zan yi. Wani lokaci idan kowa ya kwanta barci da dare, nakan tsaya in kammala wasu ayyuka saboda yin hakan na sanyawa in dan jima a gida da safe, ba sai na yi gaggawar fita wajen aiki ba da safe.
Aiki mafi sakamako gare ni
Aikin lauya zai taimaka wa mutum ya samu cimma burinsa a rayuwa. Ya taimaka mini na kasance mai zimma, wannan shi ne mafi kawo sakamako, wannar zimmar da ya cusa mini ita ta sanya na samu nasarar cimma burin da nake so. Wannan zimmar ce ta sanya na samu karfin halin neman kujerar Shugabar Kungiyar Magatakarda ta Kasa.
Burina
Koyaushe burina in zama lauya. Abin da yake burge ni shi ne shigarsu. Babbar riga mai fuka-fuki. Na samu takardar shiga jami’a har sau biyu. Na farko shi ne fannin karatun Akawu, wanda kuma shi ne mahaifina yake son in yi, saboda na iya darasin tsimi da tanadi (Economics) da kuma darasin lissafi sosai, amma sai na ki. Na shaida masa ni ba abin da nake so sai karatun shari’a. Don haka sai da na dakata har wata shekarar ta zagayo sannan na samu shiga don karanta fannin na shari’a.
Farin cikin kasancewa uwa:
Allah Ya albakace ni da ’ya’ya hudu. Biyu maza, biyu mata. Dana na farko namiji ne, kanwarsa kuma mace ce, sai kuma wani namijin wanda shi ma kanwarsa mace ce. Na farko ya kammala karatun jami’a, ya karanta fannin kudi da aikin banki, kuma a halin yanzu yana yi wa kasa hidima (NYSC). Ta biyun ma ta kammala karatu a fannin harshen Ingilishi kuma ita ma tana gaf da zuwa yi wa kasa hidima (NYSC). Na ukun kuma yana aji uku na jami’a yana nazarin Kimiyyar Siyasa. Ita kuma ’yar autata ba ta dade da gama sakandare ba, kuma tuni ta samu shiga Jami’ar Jihar Nasarawa, inda take karatu a fannin ilimin gudanar da shugabanci (Public Administration). Dukkansu ina alfahari da su kuma suna sa ni farin ciki.
Yadda na hadu da mijina
Mijina soja ne, aiki ya kawo shi Kwantagora kuma mun hadu ne wajen wani taron biki. Ga shi har mun yi aure mun hayayyafa.
Abin da ya fi burge ni game da shi
Kusan ina son duk dabi’unsa. Amma kowa ya san cewa soja ba sa daukar raini. Wannan yana daya daga cikin manyan abubuwan da suke burge ni game da shi, wanda ya yi daidai da dabi’una na lauya. Sannan yana da hakuri sosai.
Wakar da na fi so
Ina son wakokin gargajiya.
Kafar sadarwa ta zamani da nake fara dubawa da safe ko da dare
Tufafin da na fi so:
A matsayina na Bahaushiya, na fi son zannuwa.
Takalma
Ban faye son silifas ba, amma dai yanzu saboda girma ya kama ni, nakan sanya takalman da ba su da bisa kuma ba silifas ba. Amma lokacin ina ganiyar kuruciyata ina son takalma masu tsini.
Nau’in tufar da nake sanyawa a yanzu
A da can, ban faye son leshi ba, amma a yanzu da na girma na fara son sa. Don haka tufar da kawai ba zan taba sanyawa ba ita ce karamin siket.
Inda nake son kai ziyara
Ina so zuwa Dubai, kuma zuwa yanzu na ziyarce ta kamar sau biyar. Saboda akwai abubuwa masu kyau da za ka iya saya, kamar kayan sawa, sarkoki da sauransu.
Yadda nake yin hutu
Mafi yawan lokaci na fi zon in fita yawo da ’ya’yana. Amma kuma in ina son hutawa sosai sai in tsiri tafiya waje mai nisa.
Zancen hikima da ya fi burge ni
A koyaushe ina fada wa ’ya’yana cewa “Ku fadi gaskiya komai dacinta a duk inda kuka tsinci kanku.” Don na tsani karya.
Abincin da na fi so
Na fi son abinci mai nauyi amma ban faye son teba ba. Ina son amala da miyar ewedu da gbegiri. Tana da dadi sosai.
Turaren da na fi so da jakar da na fi so
Ba ni da wani zabi, ina dai son mai kyau. Ko turare ba ni da zabi na wanda na fi so, nakan so cancanjawa, ban faye son wani kamshi na dindindin tare da ni ba.
Ranar da na fi so a mako
Ina son Juma’a, saboda na san zan huta cikinta tare da iyalina, ba kamar Litinin ba. Ba na son Litinin don na san in ta zo aiki ya soma ke nan.
Shawarar da mahaifiyata ta taba ba ni da har yanzu take a raina
Maganar gaskiya ita ce, a kowane lokaci takan fada mana mu kiyayi yin karya. Wannan kuma ita ce shawarar da a kullum nake ba ’ya’yana.
Shawarata ga mata
Cewa za mu iya yin duk abin da muke son mu yi, kuma za mu iya zama duk abin da muke son mu zama. Kawai mu yarda da kanmu. Mu yi kokari mu taka kololuwa tare da yin adalci ga iyalanmu. Domin wadansu suna sanya aiki ne a gaba, su manta da iyalansu, amma ina son mata su sani za su iya hada duka biyun. Kuma ya zama tilas ki ba da gudunmawarki a wajen aiki da kuma a gida. Babu abin da zai gagara matukar dai mun sanya kanmu. Sannan gaskiya da rikon amana suna da muhimmanci kwarai.