✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ICPC ta bankado badakalar biliyoyin Nairori a shirin TSA

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce ta bankado badakalar biliyoyin Nairori a ma’akatu, hukumomi da bangarorin gwamnati karkashin shirin tsarin…

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce ta bankado badakalar biliyoyin Nairori a ma’akatu, hukumomi da bangarorin gwamnati karkashin shirin tsarin asusun ajiyar bai daya na TSA.

Shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owosanye ne ya bayyana hakan ranar Litinin lokacin da yake jawabi yayin wani taro kasa kan yaki da rashawa karo na biyu da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Farfesa Bolaji na wadannan kalaman ne a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari, da shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan, da alkalin alkalan Najeriya, mai shari’a Tanko Mohammed, da shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Dakta Kayode Fayemi da ma sauran manyan shugabannin kasa.

shi dai shirin na TSA gwamnati ta fara amfani da shi ne a shekara ta 2012 a matsayin wata hanya ta toshe zirarewar kudaden gwamnati ta hanyar tara su a asusu guda daya.

To sai dai wadannan bankade-bankaden na nuna cewa asalin makasudin shirin na fuskantar zagon kasa.

A cewar shugaban na ICPC, a binciken da suka yi daga watan Janairu zuwa 15 ga watan Agustan 2020, sun gano daga cikin ma’aikatu da hukumomin gwamnati 268, guda 72 daga cikinsu sun salwantar da biliyoyin Nairori ba tare da cikakkun bayanai ba.

Farfesa Bolaji ya ce yayin da wasu ma’aikatun suka ce sun tura N4.1bn zuwa wani asusu mai suna sub-TSA, wasu N4.2bn kuma an tura su asusun ajiyar mutane ba tare da bayani ba.

Ya kara da cewa, “Mun gano cewa an kirkiri wancan asusun na Sub-TSA ne domin a hana shirin yin aikinsa.

“Mun kuma gano wasu manyan makarantun gwamnatin tarayya da su ka kashe N2.6bn a lokacin dokar kulle da sunan ciyar da ‘yan makaranta lokacin da yaran ma suna gida amma kudaden suka zirare asusun ajiyar wasu. Mun fara bincike tuni a kan lamarin,” inji Farfesa.

Sauran badakalar da suka gano ta hada da ta karkatar da kudaden ayyuka zuwa ga asusun ajiyar na ma’aikata, kin shigar da wasu kudaden da aka karba zuwa lalitar gwamnati, aringizon albashi da ma biyansa tun kafin lokaci, yin dingishe wajen biyan haraji yadda ya kamata da dai sauransu.

To sai dai akasarin wadannan hukumomi da ma’aikatun na gwamnati sunusanta zarge-zargen inda suka ce ko dai basu da masaniya a kai ko kuma ba su suka aikata ba.