✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iceland ta kafa tarihin zuwa gasar cin kofin duniya

Iceland, kasar da mutanenta ba su wuce Miliyan 1 ba ta kafa sabon tarihi bayan ta haye gasar cin kofin duniya da za a yi…

Iceland, kasar da mutanenta ba su wuce Miliyan 1 ba ta kafa sabon tarihi bayan ta haye gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah ya kai mu.

Yanzu kasar ta sha gaban Trinidad and Tobago da ta taba halartar gasar cin kofin duniya a baya a matsayin kasar da take da karancin mutane a tsakanin kasashen da suka fafata a gasar.  Trinidad and Tobago dai tana da mutanen da yawansu ya kai Miliyan 1 da dubu 300 ne.

Trinidag and Tobago dai ta taba halartar irin wannan gasa ce mai dauke da yawan mutane Miliyan 1 da dubu 300 sai Northen Ireland da ke dauke da mutum Miliyan daya da dubu 85 sai Slobania mai mutum Miliyan 2 da dubu 8 sai Jamaika mai mutum miliyan 2 da dubu 89 sai kuma Wales mai dauke da mutum Miliyan 3 da dubu 100.

Wadannan kasashe ne suka fi karancin al’umma kuma suka taba halartar gasar cin kofin duniya a tarihin gasar. Don haka tarihi ya nuna yanzu Iceland ce ke sahun farko mai dauke da mutum kasa da miliyan1 da za ta halarci gasar ta badi a Rasha.