Duk lokacin da aka yi magana a kan yara,kowa ya san cewa abu mafi muhimmanci a gare su shi ne a ba su tarbiyya ta kwarai. Tarbiyya kuwa a takaice tana nufin kula da yaro ta hanyar koya masa duk wani abu mai kyau da kuma hana shi duk wani abu da zai cuce shi ko cutar da al’umma domin ya zama da na gari abin alfahari ga iyayensa da sauran al’umma baki daya.
Lallai iyaye su ne wadanda Allah ya dora wa kula da tarbiyyar ’ya’yansu,amma yana da matukar muhimmanci a sani cewa shugabanni da malaman makaranta da al’umma duk suna da rawar takawa a lokacin da aka yi maganar tarbiyyar yara.
Iyaye su ne makaranta ta farko a wajen yaro, don haka su dora yaro a kan hanya mai kyau .Manufa a duk lokacin da yaro ya yi ba dai-dai ba, a kwabe shi, kada a shagwaba yaro saboda kauna a kyale shi ya sangarce.Idan yaro ya yi ba dai- dai ba , a yi kokari a nuna masa cikin hikima ba ta hanyar azabtar da shi ba.Idan kuma ya yi abin kirki sai a yaba masa domin ya ji dadi ya ci gaba da yin wannan aikin alherin.
Mata yana da kyau ku kula sosai wajen tarbiyyar yara domin kuwa kun fi zama tare da yara.Yawanci a kan dora laifi a kan iyaye mata a duk lokacin da tarbiyyar yaro ta tabarbare ba tare da la’akari da cewa ba mata ne kadai suke da alhakin kula da tarbiyya ba. Wata kila shi ya sa wani lokaci idan yara suna wasa duk lokacin da yaro ya yi karya za ka ji sun ce“Allah ya tsine uwar mai karya”,ba a ambaci uba ba.To zagi dai ba abu ne mai kyau ba.Su kuma maza kada su sakar wa mata al’amuran tarbiyya baki daya,dole su sa ido su tabbatar komai yana tafiya dai-dai.
Shugabanni kuwa taimakon da za su yi wajen tallafawa yara shi ne su wadata su da makarantu kyawawa,su gina masu wuraren shakatawa ingantattu,su taimaka da asibitoci da sauran ababen more rayuwa wadanda suka kamata yara su samu domin su san cewa su ma mutane ne.Domin rashin wadannan abubuwan yakan jefa rayuwar yara da tarbiyyarsu cikin hatsari matuka.
Malaman makaranta su ma tubalai ne wajen ginin tarbiyya.Domin kuwa da zarar yaro ya tafi makaranta,to ya kamata malami ya lura da abin da yaro yake yi har zuwa lokacin tashi daga makaranta.Duk abin da yaro ya yi na ba dai-dai ba,a tsawatar masa,amma kada malami ya tsananta wa yaro domin kuwa garin neman kiba sai a samo rama.Idan malami ya takura yaro to zai tsani wannan malamin daga nan kuma sai yaro ya tsani makaranta,sai kuma ya fara daina fahimtar karatu,sai kuma fashin makaranta.Shi ke nan kuma an fara saka tarbiyyar yaro a tsaka mai wuya.
Al’umma ita ma wata makarantar tarbiyya ce mai zaman kanta, domin kuwa da zarar yaro ya dawo daga makaranta ya huta ya yi aikinsa na makaranta ,burinsa shi ne ya fita waje domin ya yi wasa da yara.To wannan abu yana da matukar hatsari domin kuwa zai iya fadawa hannun yaran banza ko manya mara sa kirki.Saboda haka yana da kyau al’umma su sa ido su tabbatar yaran unguwarsu ba sa shaye-shaye ko dauke-dauke ko bangar siyasa da sauransu.Idan kuwa har akwai irin wadannan munanan dabi’u a unguwa ya kamata al’umma su tsawatar, idan abin ya gagara sai a sanar da hukuma,tun kafin wake daya ya bata gari.
Daga karshe ya kamata iyaye da duk wanda alhakin kula da tarbiyya yake a hannunsa wanda kusan kowa yana ciki, a hadu domin hada karfi da karfe wajen kula da tarbiyyar yara,domin kuwa “Ice tun yana danye ake tankwara shi”.Idan kuwa aka bari bakin alkalami ya bushe, to al’umma za ta shiga halin “Ni ’ya su”.Saboda haka duk lokacin da yaro ya ce zai hadiyi gatari kada a sakar masa kota.