✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahimobic ya bayyana ranar da zai koma fagen daga

dan kwallon gaba a kulob din Manchester United na Ingila Zlatan Ibrahimobic ya bayyana takamaiman ranar da zai koma filin fagen daga bayan ya shafe…

dan kwallon gaba a kulob din Manchester United na Ingila Zlatan Ibrahimobic ya bayyana takamaiman ranar da zai koma filin fagen daga bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana jinya saboda raunin da ya samu.

Yanzu dan kwallon  zai fara kwallo ne a kulob din Manchester United daga ranar 2 ga watan Disamba mai zuwa. A ranar ce kulob din United zai hadu da na Arsenal a gasar rukunin firimiyar Ingila ta bana.

Shi dai Ibrahimobic tun a watan Afrilu na bana rabonsa da ya buga kwallo bayan ya samu rauni a wasan da United ta yi da Anderlecht a gasar EUROPA.

dan shekara 36, Ibrahimobic, ya sake sabunta kwantaraginsa da United ne a watannin baya, amma sai a watan Disambar bana zai fara kwallo.