✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahim Gusau ya zama sabon Shugaban NFF

Wannan dai ya kawo karshen wa’adi biyu na shekaru takwas da Amaji Pinnick ya shafe.

Alhaji Ibrahim Gusau ya zama sabon zababben Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF).

Alhaji Gusau wanda dan asalin Jihar Zamfara ne ya lashe zaben bayan samun kuri’u mafi rinjaye yayin zaben da aka gudanar a ranar Juma’a a Benin, babban birnin Jihar Edo.

A zagayen farko na zaben, Alhaji Gusau ya samu kuri’u 21 yayin da Barista Seyi Akinwunmi ya samu kuri’u 12. Sai kuma Malam Shehu Dikko da ya samu kuri’u 6 yayin da Peterside Idah da Alhaji Abba Abdullahi Yola kowannensu ya samu kuri’a daya kacal.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Dokta Christian Emeruwa da David Buhari Doherty ba su samu kuri’a ko daya ba a zaben.

Sai dai duk wannan sakamako, Kwamitin Zaben ya ayyana cewa Alhaji Gusau bai cika sharadin lashe zaben ba na samun kuri’u 22 kafin zama zababben shugaban Hukumar ta NFF.

Da wannan ne Akinwumi, Dikko da sauran suka janye takarar, amma Idah ya ce ba za ta sabu ba don sai ya ga abin da ya ture wa Buzu nadi.

Sai dai daga bisani Peterside Idah ya janye takarar, amma Kwamitin Zaben ya ce janyewar tasa na zuwa ne a kurarren lokaci, saboda haka sai an kai karshe da shi.

Bayan an gudanar da zaben a zagaye na biyu, Alhaji Gusau ya samu kuri’u 39, yayin da aka bar Idah da kuri’a daya tal.

A yanzu dai Alhaji Gusau shi ne zai jagoranci Babban Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Kwallon Kafar Kasar daga yanzu zuwa shekaru hudu masu zuwa.

Wannan dai ya kawo karshen wa’adi biyu na shekaru takwas da Amaji Pinnick ya shafe yana jagorancin Hukumar NFF.