✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibadar Aure dauke da juna-biyu

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ma’aurata da yawa sun aiko da tambayoyi game yanayin ibadar aure yayin…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ma’aurata da yawa sun aiko da tambayoyi game yanayin ibadar aure yayin da uwargida ke dauke da juna biyu, suna tambayar ko akwai hadari kuma idan akwai yaya  za a yi a kauce wa aukuwarsa? Cikin yardar Allah za mu amsa wasu daga cikin tambayoyin. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani Ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyin.
Tambaya ta 1: Don Allah yaya halaccin yin ibadar aure da mace mai juna biyu? Kuma idan ta haihu daga wane lokaci ne ya halatta a kusance ta don ibadar aure?
-Baban Khalifa, Bauchi.
Amsa: Babu wani sanannen haramci da ke tattare da kusantar uwargida lokacin da take goyon ciki, matukar an tabbatar babu wata bayyananniyar  illa da yin hakan zai haifar gare ta da kuma abin da take dauke da shi, ana iya tabbatar da haka daga wajen likitoci da malaman kiwon lafiya.
Amma idan an tabbatar yin ibadar aure na iya cutar da uwa ko abin da take dauke da shi, to bai kamata maigida ya kusanci uwargidansa a irin wannan yanayin ba, domin yin hakan kamar ya jefa rayuwar iyalinsa cikin hadari ne, kuma da gangan. Don haka haka ya kamata maigida ya ji tsoron Allah a irin wannan yanayi, ya daure ya kame kansa har zuwa lokacin da matarsa ta sauke nauyinta ko kuma har zuwa lokacin da aka tabbatar daga wajen likita cewa wannan hadarin da ka iya faruwa babu shi.
Da yawa akwai wasu mazan da ke kin bin umarnin likita, su sadu da matansu duk da sanin cewa akwai hadari, da haka har su jefa matansu cikin matsala, wata sa’in har ta kai su ga rasa abin da suka sha nauyin dauka.
Lokacin da ya halatta a kusanci uwargida bayan haihuwa kuwa shi ne, da zarar jinin bikinta ya dauke, to ana iya kusantarta matukar babu wani sauran ciwon haihuwa a ‘yanmatancinta, kuma matukar tana da isasshiyar lafiya da kuzarin gabatar da ibadar aure. Sai dai likitoci sun ba da shawarar a jira tsawon sati hudu zuwa shida kafin a ci gaba da ibadar aure bayan haihuwa, domin lokacin ana sa ran jiki ya karasa komawa daidai kuma duk wani ciwon, ko wani rauni da aka samu yayin haihuwar ya warke.
Tambaya ta 2:Tun lokacin da Allah Ya albarkaci maidakina da juna biyu, sai ya kasance ina fargabar kusantarta da ibadar aure, ina ganin kamar yin hakan zai yi lahani ga abin da take dauke da shi? Don Allah a yi mini bayani; akwai hadari ko babu?
-Kawu M, Kaduna.
Amsa: Yin ibadar aure da mai juna biyu ba ya cutar da abin da take dauke da shi matukar cikin bai kasance wanda yake tattare da wata bayyananniyar matsala ba. Domin da, yana girma a wani tsararren wuri ne, dauke cikin jakar mahaifa, zagaye yake cikin ruwan da ke hana wani abu cutar da shi, haka kuma jijiyoyin da ke tallafe da mahaifa masu karfi da tsauri ne, suna ba da kariya sosai ga dan da ke girma a cikin mahaifa. Don haka ibadar aure ko kadan ba ta da wani hadari, kuma ba ta haifar da hadari, kuma ba za ta cutar da da ba mataukar shi ainihin cikin bai zo da wata matsala ba.
Tambaya ta 3: Muna ta rigima da maigida don na ki bari ya kusance ni saboda ina dauke da dan karamin ciki, ina tsoron kada hakan ya yi sanadiyyar zubewar cikin, domin na taba yin bari sau biyu shi ya sa nake taka tsan-tsan, domin na ji an ce wai ibadar aure na iya sa karamin ciki zubewa, ko kuma a haifi bakwaini. Don Allah a bayyanar min da gaskiyar al’amarin?
Uwargidan Uthman, Abuja.
Amsa: Gaskiyar al’amari shi ne, ibadar aure kadai ba ta isa ga zama sanadiyyar zubewar ciki, sai dai idan akwai wata matsala da ke tattare da lafiyar cikin tun asali. Zubewar ciki yawanci kan faru ne a dalilin matsala a sinadaran halittar gangar jikin dan Adam (wadanda a Turance ake kira da chromosomes), amma ba a dalilin ibadar aure kadai ba. Hanyar da za ki iya gane haka sai ki je wajen likita,  don ya sanar da ke ko ibadar aure na iya zama illa ga cikinki bayan ya yi miki dukkan binciken da ya dace.
Tambaya  ta 4: Ina dauke da cikin fari ne, sai wata kawata ta gaya mini kada in rika sakin jikina sosai wajen ibadar aure, domin inzali na iya ballo mini da nakuda ko da lokaci bai yi ba? Ko maganar ta gaskiya ce?
– Daga Shagamu.
Amsa: kwarai kuwa inzali yana iya haifar da motsuwar jijiyoyin mahaifa, amma ba motsuwa irin ta nakudar haihuwa ba, motsuwa irin wacce mai ciki kan ji lokaci zuwa lokaci yayin da cikinta ya tsufa.
Tambaya ta 5: Don Allah wane yanayin kwanciyar ibadar aure ne mafi kyawu lokacin da cikin uwargida ya yi nauyi?
– Halladu
Amsa: Babu wani kebantaccen yanayin gabatarwa da za a ce shi ne mafi kyawu; wanda ya fi kyawu kuma ya fi dacewa shi ne, duk wanda ma’aurata suka fi jin dadin sa, to wannan nan shi ne daidai da su. Don haka sai ma’aurata sun saki jikinsu don su tattauna yadda za su cimma yarjejeniyar abin da ya fi sauki gare su, musamman uwargida domin ita ce ke fama da canji mai dimbin yawa a zuciyarta da kuma jikinta.