Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Ga bayani kan yadda ma’aurata za su yi amfani da ni’imomi da alheran da ke cikin Ramadan don kara zaki da dandanon soyayyar da ke tsakaninsu. Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Babu tantama, duk cikin watannin goma sha biyu, Ramadan ya fi sauran dadi ta kowane fannin rayuwa, kuma musamman ta fannin ibada. Kuzarin da ke kai kawo a Ramadan daban yake da na sauran watannin, rahma da tausayin da son bautar Allah na cika zuciyar masu imani a cikin wannan wata; dadin abin ma, ga shi an daure dukkan manya-manyan shaidanun da suka shahara wajen iya kulla kaidin mugunta da ingiza dan Adam zuwa ga aikata sabo, don haka ake ganin wadanda kafin Ramadan yin ibada ke musu wahala, sai a ga sun dage suna ta yi kamar ba su ba, hakan ke sa masallatai na cika sosai cikin Ramadan, amma da ya wuce kuma sai a koma ‘yar gidan jiya.
Aure babbar ibada ce kuma mafi soyuwa daga cikin Sunnonin Annabi SAW. Don haka kamar yadda ake dagewa wajen kyautata sauran ibadu musamman sallolin Farillah da na Nafila, sadaka da taimakon marasa galihu, to haka ya kamata a kyautata wannan babbar ibada ta aure a cikin wannan wata mai cike da albarkoki. Ma’aurata su yi amfani da wannan damar ta rahmomi da ke cike da wannan wata wajen kara dankon soyayya, kauna da zumunci a tsakaninsu ta wadannan hanyoyin:
Sabunta imani
Allah SWT Ya tabbatar mana cikin Aya ta 183 cikin Suratul Bakara cewa: “Yaku wadanda suka yi Imani! An wajabta azumi akanku, kamar yadda aka wajbta shi ga wadanda suka gabace ku domin ku zama masu takawa.”
Daga wannan aya, muna iya fahimtar cewa amfanin azumi gare mu, don mu sami takawa ne, takawa kuma ta kunshi imani da Allah da kadaita shi, ta kunshi tsoron Allah a boye da bayyane, da kuma tsarkake ibada domin shi kadai. Aure a matsayinsa na ibada kuma rabin addini ma gaba daya, ya dace a yi amfani da shi wajen samun cikakkiyar takawa a wannan wata mai albarka na Ramadan. Ga yadda ma’aurata za su yi ibadun kusantar Allah da samun karuwar imani a zuci har su kai ga dacewa da wannan takawa da Allah Ya wajabta azumi gare mu dominta:
• Gabatar da Sallar kiyamul laylinsu tare cikin kowane dare; da kuma yin addu’o’in neman biyan bukatunsu cikin wannan dare tare; maigida na rokawa uwargida na cewa amin, ko su rika roko tare.
• Yin addu’o’in neman tsari na safe da yamma tare.
• Ma’aurata su zauna kusa da kusa, hannun uwargida rike cikin hannun maigida, yayin da suke karatun Alkur’ani mai Tsarki tare, ko sauraren karatun ayoyinsa, ko daya na karantawa dayan na saurare, ko su saurari tafsirin ma’anonin ayoyinsa tare, da yin haddar wani bangare na ayoyin al-kur’ani tare.
• Yin musaffar karatun kur’ani Mai girma tare, watau kamar in maigida ya karanta ayar farko uwargida sai ta karanta ayar gaba, in ma mata biyu ne uku ko hudu, duk sai a hadu a yi tare, ana kuma iya yi har da yara duka. Wannan ya fi a zauna ayi ta kallon fina-finai da sauran shirye-shiryen talabijin marasa alfanu, kuma wannan ya fi kayatarwa da sa nishadi cikin zuciya, duk wanda ya ji ya karanta wata aya da gargada, ko ya kasa kawo ta gaba daya, to zai dage ya je ya koye ta ya ga ya iya ta. To me ya fi wannan dadi? Mutum yana tuna Ubangijinsa tare da mafi kusanci gare shi daga cikin mutane, Mala’ikun Rahma za su sauka su lullube ma’aurata da rahma, su rika sa musu albarka su na roka musu gafara, maimakon kallon fina-finai da shaidanu ne ke zama su taya su kallon. Da fatan ma’aurata za su maye dukkan wani kallon da suka saba yi, in ban da na tafsir da sauran abubuwan fadakarwa da musaffar karatun kur’ani mai Girma, ko wata ibada sassauka, amin; domin gara ma a zauna a yi hira cikin raha da irin wannan kalle-kallen.
Abubuwan kara dankon zumunci
• Bude hanyoyin sadarwa tsakanin juna: Domin sadarwa ita ke raya zumunci, kuma zumunci na tsakanin miji da mata yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu da addininsu; don haka sai ma’aurata su bude hanyar sadarwa da ke tsakaninsu sosai ta hanyar yawan zama suna tattauna abubuwan cikin rayuwarsu, matsalolinsu da hanyoyin magance su; sannan su watsar da suk wani abu da ke kawo cikas ga dorewar sadarwa a tsakaninsu, in ma wani ya yi wa wani laifi sai a yafe kuma a mance da shi. Kuma ma’aurata su zauna su rubuta burin da suke so su cim ma a cikin dangantakarsu, kuma su yi ta kokarin aiwatar da shi a cikin wannan wata da kuma bayansa.
• Yin ayyukan ibada da ayyukan gida musamman na hada abincin buda baki tare, duk abubuwa ne da za su kara dankon zumunci tsakanin ma’aurata.
• Yin buda baki waje daya, maigida ya hada iyalinsa duka, a zauna a ci abinci cikin kwano daya; yin haka zai matukar kara dankon zumunci da kaunatayya cikin iyali.
Abubuwan kara dankon soyayya
• Zuwa Sallar tarawiyy tare, kuna rike da hannun juna, kuna karatun kur’ani da ko saurare, ko yin wani zikri kamar addu’ar da ake karantawa in an kama hanyar zuwa masallaci.
• Bayan kammala gabatar da sallah, maimakon maigida ya yi tasbihi da yatsunsa, sai ya zo ya kama yatsun uwargidansa ya yi tasbihin da su, haka uwargida ma na iya yin haka.
• Maigida ya riki al’adar kullum ya rika rungumar uwargidansa kafin ya fita zuwa wajen aiki. Uwargida kuma ta riki al’adar tarbar maigida da murmushi da shiga mai kyau tare da ‘yar karamar sumba ko da a saman goshi ne ko kuma a kumatu.
• Ma’aurata su ware wani lokaci na musamman su ci abinci tare komai kankantarsa, cikin kwano daya, suna masu ciyar da junansu, kuma suna masu kallon kwayar idon junansu cikin kauna da bege, wannan zai kwararar da soyayyar juna cikin zuciya.
• A dage wurin kyautata wa juna da hakuri da juna da taimakon juna cikin wannan wata, wannan zai kara dankon soyayyar da ke tsakanin ma’aurata.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba in Allah Ya kai mu. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, Ya hada mu a kofar Ar-Rayyan, bi’iznillah, amin.
‘Ibadar Aure’ cikin Ramadan
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin.…