Ranar Lahadin da ta gabata ce aka cika mako daya da bacewar wani matashi wanda ya fita daga gida zuwa masallaci tsakanin Magariba da Isha a Layin Ibadan da ke cikin garin Kafanchan a Kudancin Jihar Kaduna.
Matashin mai suna Alhaji Suleiman Tijjani Tahir, wanda ke sana’ar citta ana kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da shi kamar yadda wani dan uwansa da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya. Ya kara da cewa babban tashin hankalin shi ne yadda har zuwa lokacin hada wannan labarin (kwana bakwai da bacewarsa) babu wanda ya san yadda aka yi ko kuma wadanne mutane ne suka yi awon gaba da shi. Ya ce suna tsammanin kiran waya kamar yadda aka san masu garkuwa da mutane na yi don neman kudin fansa amma har zuwa lokacin babu ko daya yayin da lambobin wayarsa duka suke a kashe.
Matarsa Basira Muhammad Bello ta ce bayan fitar maigidan nata zuwa masallaci wanda da zarar an idar da Sallah yake dawowa gida a ranar bai dawo ba inda da farko ba ta yi tsammanin wani abu ba, amma bayan wani lokaci sai hankalinta ya fara tashi bayan ta gwada lambobinsa ta ji su a kashe. Ta ce ta kira mahaifiyarsa ta shaida mata bisa tsammanin bai yi nisa ba, amma zuwa wani lokaci inda tare da ’yan uwansa suka dunguma suka kai rahoton bacewarsa babban ofishin ’yan sanda na garin Kafanchan. Ta ce sun tuntubi dukkan abokansa babu wani labari kuma daga bisani sun binciki manyan asibitocin garin amma babu labari.
“Mu babban tashin hankalin shi ne yadda aka shafe kwana bakwai ba shi ba labarinsa,” inji matarsa
Mahaifiyarsa Hajiya Maimuna Tijjani, wacce ta bayyana danta a matsayin mai biyayya da kula da hakkin iyaye, ta bayyana irin tashin hankalin da ta shiga na rashin ganinsa a daidai lokacinda yake shirye-shiryen tafiya aikin Umara a wannan wata na Ramadan kamar yadda ya saba.
Alhaji Suleiman Tijjani Tahir, wanda yake da mata daya da ’ya daya, shi ne Shugaban Kungiyar Ansaru Faidhatu Tijjaniyya da ke daukar nauyin gudanar da addu’ar shekara-shekara da ake yi a watan Muharram a babban masallacin Juma’a na Kofar Fadar Sarkin Jama’a da ke garin Kafanchan.