Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya ce gwamnatinsa ba za ta taba amincewa a rika kashe mutanen barkatai ba a Jihar.
Lalong ya ce gwamnatin ta yi sabuwar dokar yanke hukuncin kisa ga masu karguwa da mutane.
“Mun sanya hanu kan dokar yaki da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a jihar nan.
“A wannan doka da muka mika wa Majalisar Dokokin Jihar Filato, za a rika yanke wa duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane hukumcin kisa.”
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na jihar a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos.
Lalong ya ce sakamakon hada hannu da gwamnatinsa ta yi da hukumomin tsaron jihar, an yii nasarar samar da tabbatatcen zaman lafiya a jihar.
Ya ce suna sane da gargadin da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi, cewa wasu marasa kishi suna shirin kawo rikicin addini a kasar nan.
Ya ce don haka Gwamnatin Jihar Filato dauki gargadin da mahimmanci, tare da shirin ganin an kai rahoton dukkan wasu abubuwa na barazana ga tsaro, zuwa ga jami’an tsaro.
Ya yi kira ga al’ummar jihar kada su yarda wasu marasa kishin kasa su yi amfani da addini ko siyasa wajen raba kawunansu.
Gwamna Lalong ya yi bayanin cewa suna sane da matsalar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuffuka da ake fama da su a wasu, sassan jihar.
Don haka gwamnatinsa take haka hanu da masu ruwa da tsaki na jihar don magance matsalolin.
“Har ila yau a watan jiya, mun kaddamar da ‘yan sanda al’umma guda 595, wadanda aka ba su horo, muka raba su a dukkanin kananan hukumomin jihar nan 17,” inji gwamnan.