✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumomi na tafka kuskure game da adabi —Rahma Abdul Majid

Rahma Abdul Majid ta ce hukumomi na kuskure wajen tace adabin Hausa

Fitacciyar marubuciyar Hausa, mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, kuma mai fafutukar kare hakkin mata Rahma Abdul Majid, ta ce a yunkurinsu na kawo gyara a bangaren adabi, hukumomi na tafka kurakurai.

Malamar, wacce ta ce ta wallafa littafinta na farko ne tana da shekara 16, ta ce sanya mutanen da ba masana adabi ba ne su tace rubutu babban kuskure ne.

“Shi adabi wani abu ne da duk inda kake zato ya wuce haka…

“Kokarin a ce an sanya wadanda za su rika yi wa adabi hukunci ya zamanto kwatakwata ma ba ’yan adabin ba ne yana cikin manyan kusakuran da hukumomi suke yi – a kan iya debo ’yan siyasa, ko malamai ko wani abu a ce su ne za su iya wa adabin hukunci alhalin ba za su iya ba da zabi ba”.

Sai dai ta bayyana cewa lallai akwai bukatar hukuma ta sa ido a kan harigidon da wasu kan yi da sunan adabi.

Malama Rahma ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da suka yi da marubuci kuma dan jarida Abubakar Adam, a ci gaba da wani bikin adabin harsunan Afirka ta intanet mai suna Afrolit Sans Frontieres.

An dai fara wannan biki na adabi ne a watan Maris sakamakon ayyana dokar kulle a sassa daban-daban na Afirka, kuma Alhamis ce Ranar Hausa.

Baya ga Malama Rahama an kuma tattauna da Ado Ahmad Gidan Dabino da karfe 7 na yammacin Alhamis din.