✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Zakka a Sakkwato ta raba wa mabukata buhun gero 220

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato ta raba Naira dubu 600 da buhunan gero 220 ga mabukata…

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato ta raba Naira dubu 600 da buhunan gero 220 ga mabukata da ke fadin jihar.

Shugaban Hukumar, Malam Lawal Maidoki ne ya sanar da hakan a lokacin rabon kayan cikin harabar hukumar.

Maidoki ya ce tallafin yana cikin gudunmuwar da gwamnatin jiha ke bayarwa a duk wata don taimaka wa masu karamin karfi a birni da kauyyukan Sakkwato.

“A yau ma kamar kullum mun tsayu ne gabanku don rabon kayan tallafi daga Gwamnatin Sakkwato don taimakawa marasa karfi da masu cutar suga a kokarinta na ceton al’umma. Mabukata 200 ne zasu amfana da buhun gero 200 da kudi dubu 400, inda kowane mabukaci zai karbi naiora dubu 2 kudin mota na zuwa gida.

“Haka kuma za a bai wa mutum 20 masu ciwon suga buhun alkama daya da Naira dubu 10 kowanensu don a kara rage masu radadin ciwon. Shugaban ya yi kira ga wadanda suka samu tallafin da su aiwatar da shi yadda ya dace, kuma su yi wa wadanda suka ba su tallafin addu’a.