✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NDLEA ta kama miyagun kwayoyi a Kuros Riba

Hukumar da take yaki da fatauci da kuma shan miyagun kwayoyi ta Najeriya, wato NDLEA, reshen Jihar Kuros Riba ta ce ta kama buhunan tabar…

Hukumar da take yaki da fatauci da kuma shan miyagun kwayoyi ta Najeriya, wato NDLEA, reshen Jihar Kuros Riba ta ce ta kama buhunan tabar wiwi da miyagun kwayoyi da sauran kayan sa maye, wadanda aka kiyasta kudin sama da Naira biliyan biyu da rabi. Kayayyakin dai an kunshe su ne cikin buhunan shinkafa da kuma na takin zamani, yayin da wasu kuma cikin kwalaye.

Kwamandan hukumar na Kuros Riba, Anthonia Edeh ne ya sanar wa manema labarai haka a Kalaba.
Ya ci gaba da cewa, sun yi sa’ar kama Emmanuel Azuka a kan hanyar sa ta fita daga Najeriya zuwa kasar Kamaru da kayan a wani gari Yahe, cikin karamar Hukumar Ikom.
Da yake bayar da kiyasin adadin kayan laifin, Shugaban NDLEA na Kuros Riba Edeh, ya ce akwai kilo 76 da digo 50 na kwayoyin “Methamphetamine,” da kuma kilo 100 da digo guda na kwayoyin “Ephedrine,” da ya sanya su cikin motar daukar kaya zuwa kasar Kamaru.
Har wayau kwamandan ya ce: “Dabarar da ya yi ta badda bami, sai ya sanya kayan cikin kwalayen macaroni da taliya, wasu kuma cikin buhunan semobita, yayin da sauran kuma aka zuba su cikin buhunan takin zamani.”
karshe ya bukaci ’yan Najeriya su rika ba su bayanai na masu kunnen kashi irin wannan da aka kama.