✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NDE ta raba wa matasa 50 kayan sana’a

Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa (NDE) ta koyawa matasa 50 sana’o’in hannu tare da raba masu bashin kayayyakin sana’o’i a garin Ramin Kura…

Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa (NDE) ta koyawa matasa 50 sana’o’in hannu tare da raba masu bashin kayayyakin sana’o’i a garin Ramin Kura da ke karamar hukumar Lere ta Jihar Kaduna a ranar talatar da ta gabata.

Sana’o’in da aka koya wa matasan sun hada da gyaran wayar hannu da dinki da yin sabulai da man shafawa da saka da gyaran injin ba da wutar lantarki da aski da sauransu.
Da yake jawabi a wajen taron Shugaban Shirin Rage Radadin karin Kudin mai na Gwamnatin Tarayya wato (SURE-P) a Jihar Kaduna Alhaji Aliyu Sale Ramin Kura ya yaba wa
hukumar NDE kan yadda ta koy awa matasan sana’o’in tare da raba masu rancen kayayyakin sana’o’in. Ya ce babu shakka da irin wadannan abubuwa za a rage rashin
aikin a kasar nan. Ya ci gaba da cewa idan wadanda aka koya wa wadannan sana’o’i suka rike abin da kyau za su sami hanyar da za su taimakawa kansu da iyalansu da sauran al’umma baki daya.
Shi ma a nasa jawabin shugaban hukumar (NDE) a Jihar Kaduna Alhaji Isah Jibrin Tandama ya bayyana cewa kamar
yadda aka kafa wannan hukuma don samar wa matasa ayyukan yi wanda zai rage zauna gari banza, saboda haka aka kawo wannan tsari a wannan gari na Ramin Kura aka koya wa matasa maza da mata su 50 kananan sana’o’in hannu na tsawon watanni uku.
Ya ce: “Bayan da aka koya masu wadannan sana’o’i sai aka sayo wadannan kayayyakin sana’o’i aka raba masu a matsayin rance a wannan rana ta yau.”
Ya ce kowannensu zai biya Naira dubu 55 kuma za su dauki tsawon watanni shida suna biyan kudin. Daga nan ya yi kira ga wadanda suka amfana da wannan shiri za su rike sana’o’in
da aka koya musu da kyau domin su taimaki kansu da iyalansu da kuma sauran al’umma baki daya.
A lokacin da suke zanta da Aminiya a madadin wadanda suka amfana da wannan shiri Mista Donal Sirajo da Fatima Shehu sun bayyana matukar farin cikinsu da wadannan sana’o’i da aka koya musu. Suka ce “babu shakka an taimake su an kuma taimaki iyalansu.”
A karshe sun tabbatar da cewa za su rike wadannan sana’o’i da aka koya masu hannu biyu-biyu domin mu amfanar da kansu da sauran al’umma.